An samu fasahar kare aukuwar cutar kwalara

Yemen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fiye da mutum 2000 suka mutu sakamakon cutar kwalara a Yemen

An samu raguwar annobar cutar kwalera a kasar Yemen sakamakon wani sabon tsarin fasaha da ke yin hasashen kan alamun annobar.

Tsarin na aiki ne ta hanyayoyin amfani da hasashen ruwan sama da kuma bayanai na taswira ta hanyar kwamfuta game da muhalli da kuma yanayi.

Ana tunanin tsarin ne ya taimakawa wajen rage yawan samun cutar annobar kwalara da kusan kashi 95 cikin 100 a kasar Yemen.

Samun bayanai da suka shafi yawan al'umma da matsalar samun tsabtataccen ruwan sha da kuma hasashen yanayi ya taimaka matuka wajen magance annobar cutar a Yemen da yaki ya daidaita mutanen kasar.

Idan hasashen ya nuna alamun barkewar cutar, nan take za a gaggauta mika bayanan ga jami'an agaji wadanda su kuma za su yi gaggawar rarraba kayayyaki na tsabtace muhalli da kuma magunguna.

Hasahsen kuma ya takaita ne na makwanni hudu, inda ake kokarin tsawaitawa zuwa makwanni takwas kamar yadda Farfesa Professor Charlotte Watts jami'ar kimiyya ta sashen kula da ci gaban kasashen duniya ta Birtaniya wadda kuma ke jagorantar fasahar ta bayyana.

Ta ce suna son tsawaita lokacin hasashen daga makwanni hudu zuwa takwas, domin hakan zai ba da damar kai maganin rigakafi cikin lokaci baya ga magance aukuwar annobar.

Fiye da mutum dubu biyu suka mutu sakamakon annobar cutar kwalera a Yemen, inda yakin da ake a kasar ya haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira rikicin ayyukan jin kai mafi muni a duniya.