Kenyatta: Muna son Amurka ta kara jari a Afirka

Ana sa ran za a samu karin Amurkawa masu zuba jari a Kenya
Bayanan hoto,

Mista Kenyatta shi ne shugaba na biyu daga nahiyar Afirka da ya kai ziyara Amurka cikin shekarun nan

Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce ya shaidawa shugaba Trump ya na bukatar Amurka ta kara zuba jari a nahiyar Afirka a tattaunawar da suka yi a fadar White House.

Shugabannin biyu sun tattauna kan batun tsaro da yaki da ta'addanci da kullah huldar kasuwanci tsakaninsu.

Ana ganin China ta sha gaban Amurka ta fuskan zuba jari mai yawan gaske a Kenya.

Tun da fari a jiya litinin, mista Kenyatta ya sanar da ya fara sansano yadda kasarsa za ta samu miliyoyin daloli daga kungiyoyin Amurkawa da za su kulla kasuwanci da kasarsa.

Ya bayyana hakan ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, sannan alamu sun nuna mista Kenyatta ya na maraba da duk wanda zai kawo jari dan bunkasa tattalin arzikin kasarsa.

Ana saran mista Kenyattta zai karbi bakuncin Firai ministar Birtaniya Theresa May wadda za ta faro ziyarar aiki a nahiyar Afirka daga kasar Afirka ta Kudu.

Sannan ta yada zango kasar Kenya, bayan ziyarar ne shugaban na Kenya zai tafi birnin Beijing dan halartar taron koli tsakanin China da Afirka.