Wata yarinya ta kirkiro manhajar maganin batan yara

Wata yarinya ta kirkiro manhajar maganin batan yara

Yara na bata in sun fita yawo, hakan kuma yana tada hanakalin iyaye. Amma wata ‘yar Najeriya mai shekara 14 ta samo mafita.

Ta kirkiro wata manhaja ta wayar salula da za ta nuna inda mutum yake. Ana kiran ta “my locator”, kuma an sauke ta fiye da sau dubu daya.

Wannan labari na daga cikin shirin BBC na masu Fasahar Kirkira wato BBC Innovators, wanda Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta dauki nauyi.