An kama mutum 57 a Lagos bisa zargin luwadi

Ko a watan Yulin 2017 ma an kama wasu ''yan luwadin' 42 a Lagos.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ko a watan Yulin 2017 ma an kama wasu ''yan luwadin' 42 a Lagos.

'Yan sanda sun kama mutum 57 a Lagos da ake zargin 'yan luwandi ne.

Yan sandan jihar sun ce an kama mutanen ne a wani otal yayin da suka taru wajen wani biki na shigar da su kungiyar 'yan luwadi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Lagos Edgal Imohimi ya shaida wa manema labarai cewa, an kama mutanen ne bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu.

Kakakin rundnar 'yan sandan jihar, Chike Godwin Oti, ya tabbatar wa BBC kama mutanen.

Kuma ya ce an kama mutanen ne a lokacin da suke tsaka da shan miyagun kwayoyi da aka haramta irin su Tramadol, da tabar wiwi.

Sai dai wasu daga wadanda ake zargi sun musanta zargin.

Sun ce sun taru ne a hotel din suna bikin murnar ranar haihuwar daya daga cikinsu.

Wasunsu kuma sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN cewa rakiya kawai suka je wajen bikin, wasu kuma sun ce su 'yan rawa ne, yayin da wasu kuma suka ce abinci kawai suka kai wa masu bikin, a lokacin da aka yi awon gaba da su.

Rundunar 'yan sandan dai ta ce da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da mutanen da ake zargi gaban kotu.

Auren jinsin guda, ko luwadi ko madigo sun haramta a dokar kasar, inda a 2014 aka tanadi daurin shekara 14 ga duk wanda aka samu da laifin.

Sai dai wasu masu rajin kare hakkin 'yancin bil'adama na cikin gida da waje na sukar irin matakan da hukumomi ke dauka kan masu luwadi da madigo.