Shugabar Jamus tana zawarcin Najeriya, da Ghana da Senegal

Hakkin mallakar hoto AFP

A daidai lokacin da Firayim ministar Birtaniya, Theresa May, take ziyara a Najeriya a cigaba da ziyararta a nahiyar Afrika, wata takwararta daga Turai ita ma tana nahiyar ta Afrika.

Shugabar Jamus, Angela Merkel, tana ziyara a Senegal, kuma za ta ziyarci Ghana da Najeriya.

Shin me ya sa take ziyara? Dalilin ziyararta dai daya yake da na Misis May - bunkasa cinikayya da nahiyar Afrika.

A wani jawabin bidiyo da ta yi kwanan nan Misis Markel ta ce: "Kasashen Afrika ka iya kasancewa kyakkyawar kasuwa nan gaba."

Ta kara da cewa: "Sauran kasashe sun riga sun fara haraka da haniyar."

Da alama kowa na kokarin zawarcin Afrika , wurin da China da Faransa da kuma Amurka suka dade suna taka muhimmiyar rawa.

Yawan al'ummar da ake da su a Afirka da kuma bukatar kayayyakin amfanin yau da kullum da ake kerawa a kasashen da suka ci gaba na daga abubuwan da suka sa kasashen suke rububin Afirka.

Kasashen da suka ci gaba suna so su ci moriyar babbar kasuwar da ake da ita a Afirka da kuma damammakin kasuwanci da cinikayya.

To sai dai wasu masu sharhi na ganin ya kamata su ma kasashen na Afirka su yi amfani da wannan damar wajen gabatar da bukatun su ga manyan kasashen da suka ci gaba.

Labarai masu alaka