Jamus za ta mayar wa Namibia kokunan kai

Kokunan kai da Jamus za ta mika wa Namibia Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wakilan gwamnatin Namibia sun isa kasar Jamus don karbar ragowar kokunan kai da kasusuwan mutanen da aka harbe a zamanin mulkin Turawan mulkin mallaka fiye da shekara 100 da suka gabata.

Za dai a mika kokunan kan da kuma kasusuwa ne a wurin wani taro da za a yi a birnin Berlin.

An kai kasusuwan mutanen Jamus ne don a gudanar da binciken kimiyya da zai tabbatar da ikirarin da masu nazarin halayyar dan Adam wadanda ke nuna wariyar launin fata, ke yi na cewa Turawa sun fi bakaken fata basira da daraja.

Yawancin mamatan dubban 'yan kabilar Herero da Nama ne da aka kai su ta jirgin ruwa a shekarar 1904.

Inda sojojin mulkin mallaka na Jamus suka murkushe da karfin tsiya a lokacin boren da 'yan kabilu biyu na Namibia suka yi, inda suka hallaka dubbansu.

Ga masu tattara kayan tarihi da 'yan kasuwa da sojoji, filayen da aka hallaka mutanen da kuma sansanonin da aka tsare su, wurare ne da suka zama na kasuwanci da cin zali da azabtarwa.

Wannan dai shi ne karo na uku da Jamus ta ke mayar wa Namibia irin wadannan gawawwaki.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka