Saraki ya ayyana aniyarsa ta takarar shugabancin Najeriya

Saraki

Asalin hoton, Twitter/@BukolaSaraki

Bayanan hoto,

Tun da dai Saraki ya sauya sheka daga APC, majalisar dokokin kasar ba ta zauna ba

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya bayyana aniyarsa ta son tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019 a karkashin jam'iyyar PDP.

Saraki ya yi wannan maganar a lokacin da yake ganawa da matasa masu son yin takara, a birnin Abuja ranar Alhamis.

Ya ce kasar tana fuskantar zabi tsakanin sauya yadda take ko kuma ta cigaba da kasancewa yadda ta ke da.

Kwanan nan ne dai shugaban majalisar dattawan Najeriyar ya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki ya kuma koma PDP bayan wasu 'yan majisalr dokokin kasar kimanin 50 sun sauya sheka.

Ga bidiyon yadda ya sanar da aniyarsa ta yin takarar shugaban kasar Najeriya:

Cikin 'yan majalisar dokokin Najeriyar da suka sauya sheka din daga APC zuwa PDP akwai Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi shelar aniyarsa ta takarar shugabancin kasar ranar Laraba.

Saraki ne na baya-bayannan da ya ayyana aniyar takarar shugabancin Nigeriya a karkashin jam'iyyar PDP.

Sauran sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, da tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau, da Sanata Ahmed Makarfi.

Akwai kuma gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hasan Dankwambo, da tsohon minista Kabiru Tanimu Turaki, da Dr. Datti Baba Ahmed, da tsohon gwamnan Sakkwato Attahiru Bafarawa, da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya Kingsley Moghalu.