Alkalan Hikayata sun tantance labarai 25

Nan ba da jimawa ba ne dai za a sanar da marubuciyar labarin da alkalan suka zaba a matsayin Tauraruwar Hikayata ta bana.
A yau Alhamis alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, suka tafka muhawara don fitar da labarin da ya cancanci lashe gasar a bana.
Alkalan uku sun tattauna ne don bambance tsaki da tsakuwa a kan wadanda ko wannensu ya riga ya zaba a matsayin labarin da ya ciri tuta.
Alkalan su ne Farfesa Ibrahim Malumfashi, masani, masharhanci, kuma babban malamin adabin Hausa a Jami'ar Umaru Musa 'yar'adua da ke Katsina, da Dokta Halima Abdulkadir Dangambo, malamar adabi a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami'ar Bayero ta Kano, da kuma Hajiya Bilkisu Yusuf Ali, fitacciyar marubuciya, kuma mai sharhi a kan adabin Hausa.
Nan ba da jimawa ba ne dai za a sanar da marubuciyar labarin da alkalan suka zaba a matsayin Tauraruwar Hikayata ta bana.
Wannan ne dai karo na uku da ake shirya wannan gasa da nufin bai wa mata damar bayyana abubuwan da ke damunsu a rayuwa.
A bara dai Maimuna Idris Sani Beli ce ta lashe gasar, kuma ta samu kyautar kudi dalar Amurka 2,000 da lambar yabo.
Labaran da alkalan Hikayata suka duba:
* Aurena 12
* Alhaki
* Alheri
* Bakar Rana
* Barin Kashi a Ciki A
* Barin Kashi a Ciki B
* Da Kyar Na Sha
* Da Na Sani
* Duniyata
* Har Yanzu Ana Yi
* Illar Talla
* Kalubale
* Kulu
* Kururuwar Iblis
* Kwaya
* Laifin Suna
* Lauren Tirmi
* Matallafina
* Nadama
* Nakasa Ba Kasawa Ba
* Rubutaccen Al'amari
* Sunanmu Daya
* Waye Sila
* 'Ya Mace
* Zaina