Alkalan Hikayata na 2018 sun tantance labarai 25

Maimuna Beli, tauraruwan Hikayata ta bara.
Bayanan hoto,

Nan ba da jimawa ba ne dai za a sanar da marubuciyar labarin da alkalan suka zaba a matsayin Tauraruwar Hikayata ta bana.

A yau Alhamis alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, suka tafka muhawara don fitar da labarin da ya cancanci lashe gasar a bana.

Alkalan uku sun tattauna ne don bambance tsaki da tsakuwa a kan wadanda ko wannensu ya riga ya zaba a matsayin labarin da ya ciri tuta.

Alkalan su ne Farfesa Ibrahim Malumfashi, masani, masharhanci, kuma babban malamin adabin Hausa a Jami'ar Umaru Musa 'yar'adua da ke Katsina, da Dokta Halima Abdulkadir Dangambo, malamar adabi a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami'ar Bayero ta Kano, da kuma Hajiya Bilkisu Yusuf Ali, fitacciyar marubuciya, kuma mai sharhi a kan adabin Hausa.

Nan ba da jimawa ba ne dai za a sanar da marubuciyar labarin da alkalan suka zaba a matsayin Tauraruwar Hikayata ta bana.

Wannan ne dai karo na uku da ake shirya wannan gasa da nufin bai wa mata damar bayyana abubuwan da ke damunsu a rayuwa.

A bara dai Maimuna Idris Sani Beli ce ta lashe gasar, kuma ta samu kyautar kudi dalar Amurka 2,000 da lambar yabo.

Labaran da alkalan Hikayata suka duba:

 • Aurena 12
 • Alhaki
 • Alheri
 • Bakar Rana
 • Barin Kashi a Ciki A
 • Barin Kashi a Ciki B
 • Da Kyar Na Sha
 • Da Na Sani
 • Duniyata
 • Har Yanzu Ana Yi
 • Illar Talla
 • Kalubale
 • Kulu
 • Kururuwar Iblis
 • Kwaya
 • Laifin Suna
 • Lauren Tirmi
 • Matallafina
 • Nadama
 • Nakasa Ba Kasawa Ba
 • Rubutaccen Al'amari
 • Sunanmu Daya
 • Waye Sila
 • 'Ya Mace
 • Zaina