Mawaki Davido ya fara NYSC a Legas

Davido at NYSC camp

Asalin hoton, NYSC LAGOS FACEBOOK

Bayanan hoto,

Mawakin ya fara aikin yi wa kasa hidima ne a jihar Legas da ke kudancin Najeriya

Shahararren mawakin nan, David Adeleke Adedeji wanda ake kira da Davido yana ci gaba da jan hankalin ma'abota shafukan sada zumunta a Najeriya bayan da ya fara aikin yi wa kasa hidima wato NYSC a ranar Laraba.

Mawakin ya shiga sansanin masu yi wa kasa hidimar na unguwar Iyana Ipaja a jihar Legas.

Wajibi ne dai kowane dan Najeriya wanda bai wuce shekara 30 da haihuwa ya yi aikin yi wa kasa hidimar bayan kammala digiri da babbar difloma.

Davido ya rika wallafa hotunansa sanye da kakin 'yan yi wa kasa hidimar.

Wasu hotunan da aka ringa watsawa a shafukan sada zumunta sun nana mawakin wanda shahararren attajiri ne, tare da masu yi wa kasa hidima sun yanyame shi.