Labaran Afirka a makon jiya cikin hotuna

Zabin fitattun hotuna daga ko'ina a Afrika da na 'yan Afrika a wasu wurare a wannan makon.

Yarinya mai shekaru takwas tana tsinkar mangoro a kauyen Al-Giza na Masar a ranar Litinin 27 ga watan Agusta 2018

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yarinya mai shekaru takwas tana tsinkar mangoro a kauyen Al-Giza na Masar a ranar Litinin

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wannan manomin yana lura da 'ya'yan itatuwa da aka shirya a karkashin bishiya kafin a kwashe su don sayarwa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar talata, yara 'yan Afrika ta Kudu suna jiran Faraministar Burtaniya Theresa May ta ziyarci makarantarsu a Gugulethu

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

An yi ta yayata Theresa May bayan ta yi rawa a makarantar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Theresa May tana kai ziyara wasu kasashe uku ne a Afirka. A ranar Laraba ta gana da Muhammadu Buhari, to amma fa ba ta yi rawa ba a Najeriya. T

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A ranar kuma, shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban kasar Senegal Macky Sall sun yi Kamar za su kece da rawa, yayinda y ayi mata maraba a Dakar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An yi bikin ne fadar shugaban kasa a babban birnin Senegal inda aka tsaurara tsaro.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A babban birnin Jamus, Berlin, ranar Laraba, 'yan Namibiya sun halarci wata coci a inda aka maida kokon kan mutanen da suka mutu sakamakon kisan gilla a Namibia lokacin mulkin mallaka.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A wajen majalisar dokokin Afirka ta Kudu a ranar Jumma'a, wasu 'masu zanga-zangar adawa biyu - da masu goyon bayan Palasdinawa, da kuma masu goyon bayan Israila.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A ranar Talata, wata mata daga Jamhuriyar Demokiradiyyar Kongo ta shiga teku a karo na farko a lokacin wani shirin a Maine don taimakawa wajen tattara sababbin 'yan gudun hijirar zuwa Amurka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani dan wasa na shirin horo a kan rairayin bakin teku a Port Elizabeth a Afirka ta Kudu kafin gasar Ironman mai zuwa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar,wasu mata a Tunisia sun hau kan sikeli don gwada nauyin su a gaban wani banki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan wasa suna rawa Royal Ascot goat ranar Asabar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Tseren Awakai don tara kudi wanda yake kwaikwayon tseren dawakai na burtaniya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mata suna daukar hoto

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wani mutum yana hura vuvuzela yayin bikin ranatsar da shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa Ranar Lahadi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Nan kuma wani soja ne ya ke sauko da tutar BUrtaniya kasa ranar Alhamis bayan taron manema labarai a fadar shugaban Kenya a ranar da Theresa May ke kammala ziyarar da ta kai Afirka.

Hutuna daga AFP, EPA, Getty Images, PA and Reuters