Jamus za ta taimaki matasan Najeriya

Angla Merkle da Buhari Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Najeriya ce kasa ta karshe da Angela Merkel ta ce ke ziyarta a Afirka ta yamma

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce kasarta a shirye take ta samar wa 'yan ci ranin Najeriya halatacciyar hanya ta shiga Jamus.

Ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ranar Juma'a.

Najeriya ce kasa ta karshe da Angela Merkel ta ke ziyarta a yankin Afirka ta yamma.

Merkel ta ce tana so ta kara yawan 'yan Najeriya da ke karatu a Jamus, da a yanzu adadin ya kai mutum 1,200.

Ta kara da cewa Jamus za ta kara yawan kwararru da da ke ba da horo tsakaninta da Najeriya.

Misis Merkel da Shugaba Buhari sun ce sun amince cewa za a magance tafiya ci rani ta haramtacciyar hanya ne kawai, "idan aka samar da karin ayyukan yi ga matasa."

Haka kuma Misis Merkel ta ce za ta karfafa huldar tattalin arziki da Najeriya baya ga bangaren masana'antu.

Shugabannin biyu sun sanya hannu kan aikin noma da kera motoci, da ma kuma amincewa da samarwa manoma rance.

Misis Merkel ita ce shugabar wata kasa a tarayyar Turai da ke ziyartar kasar a wannan satin.

A ranar Laraba Theresa May ta je Abuja da birnin Legas.

Labarai masu alaka