Wasu mutane 'ba sa so a daina zub da jini a Nigeria'
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Wasu mutane ba sa so a daina zub da jini a Nigeria'

Ministan tsaron Najeriya ya ce wasu kungiyoyin kasashen waje ba sa so a daina rikice-rikice a kasar.

Mansur Dan-Ali ya shaida wa BBC cewa alkaluman da wasu kungiyoyin kasar waje ke fitar kan kashe-kashen da ake yi a Najeriya ba gaskiya ba ne.

Yana yin raddi ne game da rahoton da kungiyar hana rikice-rikice ta International Crisis Group ta fitar kwanakin baya cewa rikicin manoma da makiyaya da ya faru a jihohin Benue, Filato, Adamawa, Nassarawa da kuma Taraba ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 1300 tun daga watan Janairun 2018.

Kungiyar ta ce wadannan alkaluman sun nunka na mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram a wannan shekarar sau shida.

"Abin da mutane ba su gane ba shi ne [kungiyoyin nan] suna da tasu manufa, idan ka ga abubuwan da suke yi a Maiduguri, suna so su karfafa rikicin ya kara yawa ne, wadansu daga cikinsu ba sa son rikicin ya kare saboda a nan suke samun kudinsu," in ji ministan.

Sai dai babu wata shaida da BBC ta samu da ta gaskata wannan zargi.

Ministan ya kara da cewa bai san adadin sojojin kasar da aka kashe a rikice-rikicen da aka yi a annan shekarar ba.

Sai dai ya ce gwamnatinsu tana daukar matakai na shawo kan matsalolin tabarbarewar tsaro da ke faruwa a Najeriya.