Harin Boko Haram 'ya hallaka sojojin Najeriya 48 a Borno'

Sojan Najeriya

Asalin hoton, AFP

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa an gano karin sojoji 17 da mayakan Boko Haram suka kashe a harin da suka kai kan sansaninsu da ke Zari ranar Alhamis.

Tun da fari dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da labarin mutuwar akalla soji 31.

Sai dai a sanarwar da rundunar sojin sama ta fitar ranar Litinin ta ce dakarunta sun yi barin wuta ta sama kan mayakan Boko Haram a garin na Zari, inda suka tarwatsa su bayan sun samu rahotannin sirri.

Ita ma rundunar sojin kasa ta ce dakarunta na rundunar Operation LAFIYA DOLE sun fatattaki "mayakan Boko Haram a musayar wutar da suka yi a kauyen Zari da ke karamar hukumar Guzamala."

Amma jaridar Premiun Times, wacce ake wallafawa a shafin intanet, ta ce "an tabbatar da mutuwar akalla jami'an tsaro biyu da sojoji 48 da kuma jikkatar 19 idan aka yi la'akari da sabbin bayanan da aka samu."

Da alama dai mayakan Boko Haram masu yawa ne suka kai harin ba-zata a kan wani sansani sojoji.

Gomman mayakan kungiyar ta Boko Haram sun isa sansanin sojojin Najeriya ne a cikin manyan motoci dauke da muggan makamai.

Rahotanni sun an yi ta musayar wuta tsakanin sojojin da mayakan Boko Haram kimanin sa'a guda, kuma wani babban jami'in soji ya bayyana cewa sojoji 30 ne suka mutu a wancan lokacin.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa mayakan sun mamaye sansanin har ma sun tafi da makamai da wasu kayan yaki kafin aka fatattake su da jirgin yaki.

Wani mai magana da yawun sojojin Najeriya ya ce an kashe 'yan Boko Haram masu yawa bayan da jirgin yakin ya isa fagen dagar, inda ya rika yi musu luguden wuta.

A watan jiya ma mayakan Boko Haram sun kashe kimanin sojojin Najeriay 63 a wani hari da suka kai a yankin na arewa maso gabashin kasar.

Sanarwa: An sabunta wannan labarin