Yaushe Ali Nuhu da Adam Zango za su daina rikici?

 • Nasidi Adamu Yahya
 • BBC Hausa
Ali Nuhu da Adam Zango

Asalin hoton, Instagram

Bayanan hoto,

Wasu na ganin rikicin da jaruman biyu ke yi wasan kwaikwayo ne

Ali Nuhu da Adam A. Zango, ko kuma Sarki Ali da Prince Zango - kamar yadda aka fi sanin su a Kannywood - mutane ne masu matukar hazaka.

Baya ga basira, 'yan wasan na Kannywood na da magoya bayan da babu wani a masana'antar yake da su.

Sai dai ba magoya baya suka fi kowa kawai ba - sun fi kowanne dan wasan Kannywood yawan "munafukai" da ke kusa da su.

Watakila hakan ne ya sa suka fi ko wadanne 'yan wasan Kannywood yawan rikici a tsakaninsu.

Tambayar da kowa ke yi ita ce su wane ne wadannan mutane da ba sa so a zauna lafiya tsakanin fitattun jaruman na Kannywood? Kuma yaushe za su daina rikici tsakanin su?

Adam A. Zango, wanda ya wallafa wasu hotunansa a shafinsa na Instagram tare da Ali Nuhu ranar Asabar da daddare bayan sun kwashe wata da watanni suna "gaba", bai bayyana sunayen munafukan ba.

"Karshen munafukai...mai wuri ya dawo...Allah ina godiya da irin wadannan jarabtar da ka yi min," in ji Adam A. Zango.

Wannan dai sako ne mai cike da bayanai ga duk mutumin da ya san masana'antar Kannywood kuma ya san yadda Adam Zango ba ya yi wa bakinsa linzami.

Sai dai duk kokarin da muka yi domin samun karin bayani kan wadannan kalamai daga bakinsa ba mu yi nasara ba.

Kazalika makusantan jarumin sun ce ba su san "munafukan" da ke shiga tsakanin sa da Ali Nuhu ba.

"Wallahi ban san su [munafukan] ba," a cewar babban aminin Adam Zango, Malam Falalu Dorayi, a sakon da ya aike min na text.

Rayuwar Adam A Zano a takaice

 • An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
 • Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
 • Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
 • Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
 • Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
 • Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
 • Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
 • Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16
Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Amma Malam Muhsin Ibrahim da ke nazari kan fina-finan Kannywood kuma yake koyar da su a Jami'ar birnin Cologne ta kasar Jamus, ya shaida min cewa magoya bayan jaruman ne ke hada su fada.

"A takaice, magoya bayansu ne ke hada su rigima, kowa yana neman gindin zama."

Ba kamar Adam A. Zango ba, Ali Nuhu, ba ya fitowa fili ya bayyana wata rashin jituwa tsakaninsa da abokin aikin nasa.

Na tambaye shi ko me zai ce game da sakon da Adam Zango ya wallafa, sai ya ce "Gaskiya ba zan ce komai a kan wannan batu ba domin shi ne yake shiga kafafen sadarwa yana fadin albarkacin bakinsa, don haka ya kamata ka tambaye shi dalilan da suka sanya shi fitar da wannan sako."

Wasu masana dai na ganin hassada da girman kai ne ke sanya 'yan wasan na Kannywood biyu ke gaba da juna.

Amma Ali Nuhu ya ce "Ni ban taba fitowa fili na muzanta wani ko wata daga cikin abokan mu'amalata da kuma ina kokarin kyautata wa kowa. Amma ba zan bari na zama tamkar tabarma da za a hau kanta a wuce ba."

A baya dai fitattun masu ruwa da tsaki a masana'antar ta Kannywood irinsu shugaban hukumar tace fina-finai, Isma'ila Na'abba Afakalla da Nura Hussaini da Falalu Dorayi da Sani Sule Katsina, sun shiga tsakanin jaruman biyu amma lamarin ya ki ci ya ki cinyewa.

Sai dai Muhsin Ibrahim ya ce hanyar kadai da za a kawo karshen wannan sabani da ke yawan faruwa tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango ita ce "a hukunta masu hada su rigima."

"Manya ne ya kamata su (ƙara) shiga tsakani. A hukunta masu haɗa su rigima. Misali, bayan su Afakallah sun daidaita su a wancan lokacin, na kusa da su ne suka ƙara raba su. An san su, amma ba wani mataki da a ka ɗauka. Shi ya sa wutar ta ci gaba da ci."

Rayuwar Ali Nuhu a takaice

 • An haife shi a watan Maris na 1974
 • Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
 • Ya yi digiri a jami'ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo a 1999
 • Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci
 • Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a fina-fina Nollywood
 • Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya
 • Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa ake masa lakabi da Sarki

Da alama yanzu dai jaruman sun yi "sulhu" ba tare da an shaida wa duniya hakan ba, kamar yadda suka yi a baya.

Adam A. Zango ya taya Ali Nuhu murna bayan da fim dinsa mai suna Mansoor ya lashe kyautar fim mafi kayatarwa a gasar Africa Magic Viewers Choice Awards ta bana.

Ali Nuhu ya gode masa, abin da masana Kannywood ke ganin wata alama ce ta dinka barakar da ke tsakanin su.

Asalin hoton, @Instagram/Muhsin Ibrahim

Bayanan hoto,

Masu bibiyar jaruman na fatan ba za su sake kai ruwa rana ba

Sai dai wasu na gani ba rikici Ali Nuhu da Adam A. Zango ke yi ba, illa dai suna wasa da hankulan masu bibiyarsu.

"Duk abin da kuka ga suna yi suna sane kuma su suke kirkirar hakan don kar a ce ai kwana biyu an manta da su, to ku sani ku masoyansu ku suka mayar mahaukata.

"Idan baku manta ba a shekarun baya sun taba shirya irin wannan rikicin nasu muka zo muka yi ta ce-ce-ku-ce a kai amma daga karshe suka mayar da mu bamu san komai ba," a cewar Ali Artwork, wani matashi mai barkwanci a masana'antar Kannywood, a lokacin da suka samu rashin jituwa a shekarar 2017.

Ko ma dai mene ne gaskiyar abin da ke faruwa a tsakanin Ali Nuhu da Adam Zango, masu sha'awar fina-finansu za su yi murnar ganin sun hada kan su domin su fuskanci manyan matsalolin da Kannywood ke fama da su.