An kai mummunan harin bam a birnin Mogadishu

A photo showing the aftermath of the blast, with people standing in front of rubble

Asalin hoton, Twitter/@abdi_adaani

Bayanan hoto,

Ganau sun ce harin ya lalata gine-gine da dama

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan jami'an gwamnati a Mogadishu, babban birnin Somalia, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla sojoji uku.

Jami'ai sun shaida wa BBC cewa akalla mutum 14 sun jikkata, cikin su har da kananan yara shida sannan ginin wata makaranta ya rufta saboda karfin harin.

An kai harin na mota ne a lardin Howlwadag.

Harin ya lalata wasu gidaje sannan ya yaye rufin wani masallaci da ke kusa.

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta al-Shabab, wacce ta kashe sama da shekara goma tana kai hare-hare a kasar, ta dauki alhakin kai harin.

Wani dan sanda Abdullahi Hussein ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa dan kunar bakin waken ya doka motar shake da bama-bamai kan ofishinsu da ke Howlwadag.

Tun shekarar 1991 Somalia ke fama da tashe-tashen hankula, lokacin da aka kifar da gwamnatin sojin kasar.

Asalin hoton, Twitter/@abdi_adaani

Bayanan hoto,

Harin ya lalata wani masallaci

Asalin hoton, A H Baliil

Bayanan hoto,

Soji uku ne suka mutu sanadin harin

Tumbuke gwamnatin Mohamed Siad Barre ya yi sanadin yakin basasa tsakanin kungiyoyin da ba sa ga-maciji da juna na shekara da shekaru, sannan lardunan kasar biyu - Somaliland da Puntland - suka balle daga Somalia.

Akasarin kasar ta koma tamkar filin yaki.

A 2012 ne aka kafa gwamnatin da majalisar dinkin duniya ke mara wa baya. An kori yawancin mayakan Al-Shabab zuwa yankunan karkara sai dai har yanzu suna iya kai hare-hare a ofisoshin gwamnati a babban birnin kasar.

Asalin hoton, Twitter/@saxafi111