Kun san kasar da aladu za su fi mutane yawa?

  • Labarai daga wasu wurare...
  • ...BBC Monitoring
Lots of pigs at a sty in Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yanka alade 50m a Spain a 2017

Sabbin alkaluman aladun da ake yankawa a Spain sun sanya an soma bayyana fargaba a kafafen watsa labarai cewa watakila nan gaba kadan aladu za su fi mutane yawa.

Ma'aikatar muhallai ce ta fitar da alkaluman a wannan makon inda ta ce a shekarar da ta gaba an yanka aladu 50m - yayin da al'umar kasar ba su wuce mutum 46.5m ba.

Wannan lamari ya sanya jaridun kasar na nuna fargaba cewa aladun kasar sun zarta mutanenta yawa. Sai dai jaridar Euronews, ta ba da rahoton da ke cewa mutanen Spain sun fi yawan aladun kasar da kimanin 16m a lokaci guda, inda ake yanka wasu daga cikin su jim kadan bayan an haife su.

Amma duk da haka ana bayyana fargaba a kasashen da ke tarayyar turai cewa yawaitar karuwar kiwon alade ka iya sanya wa su zarta adadin mutanen nahiyar.

A halin da ake ciki dai, Denmark ce kasar turai da aladunta suka fi mutanenta yawa, inda alkaluman da Eurostat ta fitar a 2016 suka nuna cewa a duk inda aka samu mutum 100, to ana samun aladu 215. Al'umar Denmark sun kai 5.7m, abin da ke nufin, a kiyasce akwai alade 12.3m a kasar.

Kazalika akwai aladu masu tarin yawa a Netherlands, Spain da kuma Belgium wadanda suke gogayyar ganin sun kai adadin mutanen kasashen.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kiwon alade ya ninka sau biyar a Spain a shekarun baya bayan nan