Ba na tsoron fafatawa a zabe na gaskiya — Buhari

Gwamnan jihar Lagos, wanda ake rade-radin cewa zai fice daga APC, na cikin tawagar Shugaba Buhari

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Lagos, wanda ake rade-radin cewa zai fice daga APC, na cikin tawagar Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba ya tsoron fafatawa a zabe idan za a gudanar da shi cikin gaskiya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin ganawa da 'yan Najeriya mazauna kasar China a birnin Beijing inda yake ziyara.

A cewar sa, "Ba na jin tsoron karawa a zaben da za a gudanar cikin gaskiya saboda shi ne ya sa na zama shugaban kasa. Na san irin faman da na yi inda sau uku ina tsayawa takara ina faduwa zabe amma ina kalubalantar sakamakon sa a kotun koli."

"Da na fadi a zabe karo na uku na ce 'Allah ya saka min'; daga bisani aka yi amfani da fasahar na'ura wuririn gudanar da zabe kuma hakan ya taimaka mana,' in ji Shugaba Buhari.

Shugaban na dai ya ayyana sha'awarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a jam'iyyar APC mai mulki.

Ya ce zai sake tsayawa takarar ce domin ya kammala aikinsa na ci gaban kasa.

Sai dai ra'ayoyi sun sha bamban game da ayyukan da Shugaba Buhari ya ce ya yi.

Wasu 'yan kasar na yabonsa bisa yaki da rashawa da cin hanci da matsalar taro, ko da yake wasu na ganin ya gaza fitar da kasar daga kangin tattalin arzikin da take ciki.

Kazalika babbar jam'iyyar hamayya da wasu 'yan Najeriya na cewa Shugaba Buhari yana yaki da cin hanci ne kawai kan 'yan adawa, inda yake kau da idanunsa kan 'yan jam'iyyarsa ta APC da kuma wadanda suka kira shafaffu da mai.

Idan APC ta tsayar da shi takara, Shugaba Buhari zai fafata da watakila tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Kwankwaso, gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ko dai duk mutumin da PDP ta tsayar takara a zaben 2019.