Shin ya kamata Afrika ta yi dari-dari da karbar bashi daga China?

  • By Larry Madowo
  • Editan labaran ciniki, BBC Afirca
Ma'aitakan China a Kenya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ma'aitakan China a Kenya

Kasashen Afirka na nuna alfanun kudaden bashin da suke karba daga China, duk da cewa masana na nuna damuwarsu a kan karuwar wadanan basusuka da ake hasashen cewa nan gaba za su iya zama alakakai a nahiyar.

Babban titin Entebbe-Kampala har yanzu na jan hankalin masu zuwa yawon bude ido Uganda, kusan wata uku da bude shi.

Titin mai tsawon kilomita 51 da motoci hudu ke iya jeruwa kafada da kafada, ya hade babban birnin kasar da tashar jirgin Entebbe, da wani kamfanin China ya gina a kan dala miliyan 476 a matsayin rance da aka karbo daga Bankin Exim na Chinar.

Titin ya kawo sauki da takaita tafiyar sa'a biyu zuwa minti 45 a hanyar da a baya ke yawan fuskantar cunkoson ababen hawa a birnin da ke gabashin Afirka.

Bayanan hoto,

Sabon katafaren titin da aka kashewa milyoyin dalolin kudadden da aka samo rance daga China

Uganda ta karbi bashin dala biliyan Uku daga China wanda masanin tattalin arzikin kasar Ramathan Ggoobi ya ce ''an zuba jarin da babu irin sa a Afirka''

''Wannan bashi da China ta bayar zai habaka cinikaya tsakanin kamfanonin kasar, musaman kamfanonin gine-gine da suka dukufa wajen ginin layin-dogo da tittuna da madatsun ruwa da ake samar da wutar lantarki da filayen wasanin da gine-ginen wurin harkokin kasuwanci da dai sauransu,'' kamar yadda jami'ar kasuwanci ta Makerere ke shaidawa BBC.

Karbar wadanan kudade bashi daga China na zuwa ne adaidai lokacin da kasashen Afirka da dama ke sake tsunduma a cikin barazanar basussuka.

Akalla kashi 40 cikin 100 na kasashen nahiyar da ke fuskantar karancin kudaden shiga na cikin kangin bashi da sauran matsalolin tattalin arziki, kamar yadda hukumar bada lamuni ta duniya, IMF ta yi gargadi a watan Afrilu.

Bayanan bidiyo,

China ta shirya zuba hanayen jarin $60bn a Afirka kafin karshen shekara ta 2018.

Tun a shekara ta 2017 ake yi wa irinsu Chadi da Eritrea da Mozambique da Jamhuriyar Congo da Sudan ta Kudu da Zimbabwe kallon kasashen da ke fama da matsalolin basusuka, yayin da Zambia da Ethiopia ake bayyanasu da kasashen da barazanar basusukan ta fi yawa.

''A 2017 kawai, yawan yarjeniyoyin da China ta sanya hannu da Afirka ya kai dala biliyan 76.5,'' kamar yadda Jeremy Steven masani tattalin arziki da kuma ke aiki da Banki Standard na China ya wallafa.

''Sai dai, duk da girman gibin da ake da shi a nahiyar, akwai damuwar cewar wadanan basusuka da kasashen Afirka ke karba za su ragu,'' a cewar Jeremy.

Kamfanonin China na samun goyon-bayan manyan mutane daga nahiyar Afirka, irinsu shugaban Bankin bunkasa Afirka (ADB) Akinwumi Adesina, tsohon ministan noma a Najeriya.

''Mutane da dama na tsoron China amma ni ba na tsoro. A gani na China kawar Afrika ce,'' a cewar Adesina a hirarsa da BBC.

China yanzu ta sha gaban kowa wajen zuba kudaden a fanin gine-gine a Afirka, ta kuma sha gaban Bankin ADB da Hukumar Tarayyar Turai da Bankin zuba jari na Turai da Bankin Duniya da Kungiyar Kasashen nan 8 masu karfin tattalin arziki wato G8.

China - 'Nasarorinta'

Tasirin kudadenta a bayyane ya ke a duk fadin Afirka, kama daga sabbin filayen jiragen sama da tittuna da kuma tashoshin jiragen ruwa da dogayen gine-gine wanda ke samar da ayyukan yi.

Binciken McKinsey da masu sharhi kan kamfanoni, sun gano cewa kudaden rancen da Beijing ta ba wa Afirka sun rubanya tun daga 2012, ciki harda da dala biliyan 19 da aka ba wa Angola a 2015 da 2016.

Sai dai an bayyana Angola da Zimbabwe a matsayin kasashen da babu daidaito tsakaninsu da China a Afirka.

Bayanan hoto,

Ana ta samun kace-nace akan kudaden hannayen Jarin da China da Zuba a Zambia

''Gwamnatin Angola na ba wa China man fetur don musayar kudi da kuma cin gajiyar manyan ayyukan gine-ginen- sai dai yanayin kasuwaci na takaita zuba jari daga 'yan kasuwar China a Angola, idan aka kwatanta da sauran kasashen Afirka,''

Afirka ta samu riba sosai a fanin cinikayya, da zuba jari da tsarin kudade tsakaninta da China, a cewar wani dan kasar Ghana mai sharhi akan zuba jari Michael Kottoh.

''Sai dai abu ne a zahiri cewa China na samun nasara-la'akari da yadda take cimma akasarin yarjeniyoyinta.''

McKinsey ya yi hasashen cewa kudadden shiga na kamfanonin China a Afirka zai iya kai wa dala biliyan 440 kafin 2025.

Ko Mista Adesina ya yarda cewa: ''Abinda na ke gani shi ne, rashin daidaito a yarjeniyoyin, inda ka ke bayar da 'yancin ka na hakar ma'adini saboda kawai kana son a gina ma ka kayataccen titi.

''kana harka da kasa guda, ta ya ya ka ke da tabbacin cewa yarjejeniyar da ka ke son a cimmawa ta fi kowanne?''

'Ganin Kyashi'

Ba a taba samun rahoto ko halayyar rashawa na ketare akan China ba kamar Amurka, ko irin wannan dabi'a a sauran kasashen yamma da suka haramta karbar toshiya da sunan samun kwangila.

Ko da ya ke masanin tattalin arziki nan da ya taba lashe kyautar karramawa ta Nobel, Joseph Stiglitz ya bayyana sukar da kasashen Yammacin duniya ke yi wa China kan mu'amalarta da nahiyar Afirka a matsayin "ganin kyashi"

''Kowanne irin aiki da aka samu ko daga China ko kasashen yamma na bukatar nazari da ribar da zai kawo,'' ya kuma shaidawa BBC a Nairobi cewa zabi ya rage ga gwamnatocin nahiyar kan gudanar da ayyukansu a bayyane.

Wasu Karin labarai akan China:

Mista Ggoobi ya kuma shaida cewa akwai damuwa sosai akan tasirin da muhalli ke yi akan zuba jarin China, ''musamman akan talakawa, masu rauni da hukumomin da ke yakar rashawa a Afirka.''

A 2015, wani shirin da ke nazari akan alakar China da Afirka na jami'ar Johns Hopkins ya yi gargadin cewa nan gaba akwai yiwuwar kasashen Afirka su gagara biyan basussukan da suke karba daga China saboda '' matsalolin rashin daidaiton firashi da koma bayan bijiro da sabbin dabaru.''

''Mun gano cewa rancen da ake karba daga China ba su ke haddasa karuwar matsalolin basusuka a Afirka ba,'' sun shaida haka ne gabannin taron hadin-kan China da Afirka da ke tafe a cikin wannan mako a Beijing.

China tana da gagarumin hanayen jari a Afirka, sai dai kasashen na kuma karbar rance daga wasu wuraren na daban don haka ba ita kadai za a daurawa girman wadanan basusuka ba.

A ganwarsu ta baya a Johannesburg, China ta alkawarta bada tallafin rancen dala biliyan 35 a Afirka.

Abin da ba a samu cigaba ba shi ne batun da Bankin Standard ya bayyana da ''gibin cinikayya da China'' tun 2015. Ya ce kasashen Afirka biyar kacal ne ke samun sama da abinda suka bukata na kasuwanci daga China.

Mr Ggoobi na son China ta taimakawa Afirka a gina cibiyar da za ta ja hankali da dawaniyar zuba jari ta hanyoyin amfani da kebabbun yankunan da za su samar da tattalin arziki da samar da masana'antu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugabannin Afirka na taro kowacce shekara a hedikwatar da China ta samar akan $200m a Ethiopia

A watan da ya gabata Djibouti ta kaddamar da kashin farko na yankin kasuwanci mara shinge na China wanda aka bayyana da mafi girma a Afirka, sai dai ana kallonsa a matsayin wani bangare na kokarin da China ke yi na mamaya ta hanyar farfado da tsoffin hanyoyin kasuwancinta da shirinta a kasashen Afirka 60.

'Yan Uganda na iya cin moriyar katafaren sabon titinsu a yanzu, sai dai akwai fargabar su iya karkarewa ko nutsewa a cikin kangin bashin China.