Theresa May: 'Tarayyar Turai ba ta amince da shirina na Brexit ba'

Babban jami'i da Tarayyar Turai game da ficewarta daga Tarayyar Michel Barnier Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Babban jami'i da Tarayyar Turai na Brexit Michel Barnier

Babban jami'i Na Tarayyar Turai game da ficewarta daga Tarayyar, Michel Barnier, ya ce bai amince da wasu daga cikin shawarwarin da Firai minista Theresa May ta mika ba dangane da dangantakar kasuwanci da cinikayya tsakanin bangarorin biyu.

Amma Firai ministar ta kafe cewa ba za ta sauya matsayin gwamnatinta ba.

Duk da cewa Mista Barnier ya sha sukan tsarin gwamnatin Birtaniya dangane da samar da wata sabuwar dangantaka bayan Birtaniyar ta fice daga Tarayyar ta Turai, amma bai taba fitowa fili yana sukar ta ba kamar haka.

Ita kuwa gwamnatin Birtaniya ta mayar da martani, inda ta bayyana cewa matakan da take son dauka za su zama masu alfanu gareta har da ma Tarayyar Turan.

An shirya kammala dukkan tattaunawa game da batun ficewar Birtaniyar ne a watan Oktoba, amma Mista Barnier na ganin jinkirin da ake fuskanta na iya kai batun har zuwa watan Nuwamba.

Gwamnatin Birtaniya a karkashin Theresa May ta kasa samar da wata matsaya da za ta gamsar da Tarayyar ta Turai har ma da yawancin 'yan kasarta game da hanya mafi dacewa da za abi wajen rabuwa da Tarayyar Turai.

Wannan ya janyo mata bakin jini matuka, inda har jam'iyar Labour mai adawa da gwamnatin kasar ke kallon wannan batun a matsayin wanda ka iya zama mata dama da za ta kayar da 'yan Conservatives a babban zabe da ke tafe.

A karshen watan Maris na 2019 ne Birtaniya za ta fice baki daya daga kungiyar Tarayyar Turai, amma kawo yanzu babu wanda ya san ko hakan zai yiwu.