An yi taro a kan rayuwar marigayi Mamman Shata a fagen waka

Mamman Shata Katsina da 'yan amshinsa

Asalin hoton, BAKANDAMIYA.COM

An yi wani taron masana a kan rayuwar marigayi Dr Mamman Shata da basirarsa a fagen waka a Najeriya ranar Litinin.

Masana daga kasashen duniya ne za su gabatar da makala a wajen taron, wanda Cibiyar nazarin harsunan Najeriya ta shirya, tare da hadin gwiwa da Sashen Nazarin harsunan Najeriya da kuma sashen Nazarin kimiyyar harshe na jami`ar Bayero ta Kano.

Bayanan hoto,

Sanusi Shata wanda dan autan marigayin ne shi ma ya halarci taron

Taron dai yazo ne a daidai lokacin da wasu ma`abota tsofaffin wakoki irin na shata da dangoginsa ke kukan cewa kafafen yada labarai na mai da su saniyar-ware a filayen shakatawa da suke gabatarwa a cikin shirye-shiryensu.

Bayanan sauti

Wakar Nura M Inuwa ta Ranar Aurena

Wannan na faruwa ne, kasancewar hankalinsu ya fi komawa kan mawakan nanaye, suna fargabar cewa irin hkima da azancin da ke cikin tsofaffin wakokin ka iya bacewa idan aka ci gaba da tafiya haka.

Ma`abota wakokin tsofaffin makadan na da ra`ayin cewa wakokin magabatan na cike da darusan da suka shafi adabi da harshe, don haka wakoki ne da bai kamata a yi wasu da suba.

Alhaji Musa Danbirni, mai sha'awar zallar wakokin marigayi Alhaji Mamman Shata ne, har ta kai ga Shatan ya masa waka:

"Makadan da suka fi burge ni yanzu babu su. Kayan kida da suka bace sun hada da molo, akwai garaya, akwai kuntigi da dundufa. Sannan akwai kotso da kalangu."

Ya kara da cewa, "Duk kida ne da ake yi a da a zuga mutum da 'ya'yansa. A fadi sarautarsa idan mai sarauta ne, kuma a fadi kasuwancinsa idan dan kasuwa ne."

Ya kuma bayyana sunayen wasu mawakan na dauri da suka burge shi:

"Akwai hikima da azanci da balaga da Allah ya ba su akwai Dan Anache, da Sarkin Taushin Katsina, da Aliyu Dan Dawo da Mamman Shata. Akwai kuma Haruna Uji da Ali Makaho da Dan Maraya Filato."

Ya ce dukkansu sun kaura kuma babu su babu irinsu.