'Yanmata na cikin hadari a yankin Tafkin Chadi

Kungiyar ta ce yara mata a yankin, ciki har da wasu sassan Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru, na rayuwa cikin tsananin tsoro.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyar ta ce yara mata a yankin, ciki har da wasu sassan Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru, na rayuwa cikin tsananin tsoro.

Wata kungiya mai rajin kare hakkin kananan yara ta Plan International, ta yi gargadin cewa 'yanmata da ke zaune a yankin Tafkin Chadi a yankin yammacin Afirka na cikin hadarin fuskantar gallazawa daga mayakan Boko Haram da kuma al'ummominsu.

Kungiyar ta ce yara mata a yankin, ciki har da wasu sassan Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru, na rayuwa cikin tsananin tsoro.

Yara matan da a ka yi binciken da su, sun fuskanci cin zarafi kala-kala ciki har da gallaza musu a gidajensu. Kusan kashi daya bisa hudu na wadanda a ka gudanar da binciken a kansu sun bayyana cewa an buge su a cikin watan da ya wuce.

'Yan matan dai na cikin hadarin yiwuwar sace su da yi musu fyade da kuma yi musu auren dole daga mayakan boko haram da ma mutanan da su ke yi wa aiki a matsayin 'yan aikatau.

Kungiyar ta ce iyalan yaran da a ka yi wa fyade na nuna musu kyama, inda hakan ke tursasa musu shiga karuwanci.