'Mun fi karfin PDPn Abuja ta yi mana korar kare'

Asalin hoton, PDP
Dubban magoya bayan PDP ne suka yi zanga-zanga a Kano
Dubban magoya bayan jam`iyyar PDP, masu mubaya`a ga manyan jagororin gidaje uku a jihar Kano sun yi wata zanga-zanagar nuna goyon baya ga shugabancin jam'iyyar na Kano, wanda uwar jam'iyyar ta kasa ta bayar da sanarwar rusawa a makon jiya.
Masu zanga-zangar da suka yi ikirarin cewa sun fito ne daga dukkan kananan hukumomin jihar 44, sun taru ne a hedikwatar jam`iyyar ta jiha don nuna rashin jin dadinsu da matakin da uwar jam`iyyar PDP ta kasa ta dauka.
A yanzu dai a iya cewa wani sabon rikici ya kunno kai a cikin PDP reshen Kano, mai fatan kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC.
Yayin da shugabannin ke cewa ba su rusu ba, wasu gidajen jiga-jigan jam`iyyar su ma sun ce ba su yarda da rusa shugabannin nasu ba.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa sai da aka bi dukkan ka`idoji wajen zabar shugabannin nasu, don haka rusa su da uwar jam`iyyar PDPn ta yi salo ne na kama-karya, kuma ba za su amince da shi ba.
Su ma shugabannin jam`iyyar PDP na jihar Kano, wadanda uwar jam`iyyar ta ce ta rusa, sun ce har zuwa yammacin Litinin wai-wai kawai suke ji.
Mataimakin shugaban jam`iyyar PDP na jihar Kano Alhaji Ibrahim Muhammad KT ya ce babu wata shaida da uwar jam'iyyar ta ba su.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Ya ce kuma ko da an ba su takarda, to ba su rusu ba, domin kuwa jama'a ne suka zabe su, ba uwar jam'iyyar ce ta nada su ba, "don haka sun fi karfin a yi musu korar kare," in ji Alhaji Ibrahim KT
Tun a ranar Asabar da ta wuce ne hedikwatar jam`iyyar PDP ta kasa ta sanar da rusa shugabannin jam`iyyar na Kano, amma ba ta gabatar da wani hanzarin da ya sanya ta daukar matakin ba.
Sai dai wasu na da yakinin cewa ta yi haka ne da nufin sake yi wa shugabancin garambawul ta yadda za a dama da bangaren tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi`u Musa Kwankwaso, wanda ya sauya-sheka zuwa jam`iyyar kwanan nan.
Tun dai komawar Senata Rabi`u Musa Kwankwaso da jama`arsa jam`iyyar PDPn wasu masana da abokan hamayyar jam`iyyar ke cewa da wuya tafiyar ta dore, suna jaddada cewa za a ji kansu wajen rabon shugabanci.
Kuma zancen da ake yi, wata ruwayar na cewa bangaren Kwankwaso ya nemi kashi hamsin da daya cikin dari na mukaman jam`iyyar, tare da ba wa bangarensa da ke kan kujeru a majalisar dokokin jiha da ta tarayya damar zarcewa, yayin da sauran gidajen kuma za su raba ragowar kashi 49 a tsakaninsu, abin da kuma aka ce hakan ne ya kawo rashin jituwa cikin jam'iyyar a jihar.