An kirkiro kayan saukaka wa mata hadarin haihuwa

An kirkiro kayan saukaka wa mata hadarin haihuwa

A yankin kudu da hamadar sahara na Afirka, mata da jarirai na mutuwa yayin haihuwa fiye da ko ina a duniya.

To amma wata matashiya mai basira ta yi tunanin cewa akwai mafita.

Tana kiran wasu kaya da ta samar kayan haihuwa ga iyaye, wasu kaya ne masu muhimmanci domin hana iyaye da jarirai mutuwa yayin haihuwa.

Wannan labari na daga cikin shirin BBC na masu Fasahar Kirkira wato BBC Innovators, wanda Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta dauki nauyi.