Ma'aikaciyar BBC Rachael Bland ta ce 'kwanaki kadan' suka rage mata a duniya

Rachael Bland
Presentational white space

Rachel Bland mai gabatar da labarai a shirin 5 Live na gidan rediyon BBC ta bayyana a shafukan sada zumunta cewa tana da sauran kwanaki kafin ta mutu.

Likitoci sun gano matar mai shekara 40 da haihuwa tana da cutar daji a mamanta a watan Nuwambar 2016.

A watan jiya ta bayyana cewa tana saurin kammala rubuta wani littafi domin dan ta mai suna Freddie, kuma mai shekara biyu da haihuwa ya karanta bayan ya girma.

Ta bayyana cewa ta tabbatar ba za ta shekara ba kafin mutuwa ta riske ta.

Rachel mai karanta labarai ce, kuma ta kan gabatar da shirin You, Me and the Big C tare da Deborah James and Lauren Mahon.

A ranar Litinin, ta aika da wani sakon Twitter, inda ta ce abokan aikin nata biyu za su cigaba da gabatar da shirin bayan ta mutu.

Ta rubuta sako cewa: "Kamar yadda shahararren mawakin nan Frank S ya ce - Ina sanar da ku abokai na cewa lokacin ya karato. Kuma kwatsam ya iso.

"An sanar da ni cewa kwanaki kalilan suka rage min. Abin tamkar mafarki. Ina mika godiya ta a gareku saboda karfafa min gwuiwa da kuka rika yi."

An haifi Rachel a birnin Cardiff ne, amma tana zaune ne a Cheshire na kasar Ingila. A watan Mayun bana aka sanar da ita cewa babu magani ga cutar dajin da take fama da ita.

Amma bayan wata biyu sai bincike ya nuna wa likitoci cewa cutar ta kara bazuwa zuwa wasu sassa na jikinta.

Asalin hoton, Rachael Bland

Bayanan hoto,

Rachael Bland tare da mijinta Steve

Abokiyar aikinta a shirin 5 Live ta aika mata da sako, inda ta ce: "Kin zama mace mai ban al'ajabi a gareni. Ina mika kaunata ga kowa."

Shi ma abokin aikinta, Tony Livesey wanda ke gabarta da shirin 5 Live Drive ya aika mata da sako a shafinsa na Twitter: "Wannan irin karfin zuciya da kike da shi. Jinjina ga matar da ta fara nuna min yadda aiki yake a @bbc5live, ina so ta sani cewa muna tare da ita a daidai wannan lokacin.

Sauran abokan aikinta ma ba a barsu a baya ba:

Asalin hoton, Claire Wood

Bayanan hoto,

Rachael Bland ta kan gabatar da shirin You, Me and the Big C tare da Deborah James and Lauren Mahon