Shugaba Xi na China ya ce ba domin fariya su ke taimakawa Afirka ba

President Xi Jinping gives a speech during the opening ceremony for the Forum on China-Africa Cooperation at the Great Hall of the People in Beijing on September 3, 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban China ya ce zuba jari zai amfani Chinar da Afirka

Shugaban China Xi Jinping ya kare shirin kasarsa na zuba jari a nahiyar Afirka, inda ya ce shirin zai amfani Chinar da Afirka.

Ya kuma ce ba domin dalilan siyasa ake gudanar da ayyukan raya kasa a nahiyar ba.

Shugaba Xi na magana ne a yayin wani taron koli tsakanin China da Afirka a Beijing.

Shugaba Xi Jinping ya ce hadin kai tsakanin Chna da Afirka na kawo cigaban nahiyar matuka.

Amma akwai damuwar cewa wasu kasashen Afirka sun fada tsundum cikin ramin bashi da Chinar ke samarwa.

China na bai wa kasashe masu tasowa biliyoyin daloli domin ayyukan raya kasa kamar hanyoyin jirgin kasa da na mota.

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya yi watsi da wannan batun, kuma ya ce muhimmancin dangantaka tsakanin Afirka da China na karuwa musamman ma a yanzu da wasu kasashen ke kokarin biyan bukatun kansu ne kawai.

Shugabannin kasashen Afirka da dama na kallon kasashen yammacin Turai da Amurka ba su damu da cigaban kasashensu ba.

Asalin hoton, Getty Images

Shugabannin sun ce yunkurin kasashen yamma na fadada karfin fada a ji da suke yi a fagen siyasa da tattalin arzikin duniya ba zai sami karbuwa ba a nahiyar Afirka.