Tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya fice daga PDP

Shekarau da Kwankwaso

Asalin hoton, @KWANKWASORM

Bayanan hoto,

Masana siyasa sun ce da ma da wahala Shekarau da Kwankwaso su zauna a inuwa guda

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekaru ya fice daga jam'iyyar PDP.

Da asubahin Talatar nan ne Shekarau ya bayyana ficewa daga PDP, a cewar mai magana da yawunsa Malam Sule Ya'u Sule.

Shekarau, wanda yana daya daga masu neman takarar shugabancin Najeriya a jami'iyyar PDP ya ce ya fice ne daga jam'iyyar saboda zargin rashin adalci a bangaren shugabannin jam'iyyar na kasa, wajen rushe shugabancin jam'iyyar na jihar Kano, da yunkurin mikawa Kwankwaso shugabancin.

A ranar Litinin ma wasu dubban yan PDP a Kano sun yi wata zanga-zangar nuna adawa da matakin uwar jam'iyyar.

Shekarau ya ce gabanin daukar wannan mataki, sai da suka zauna da shugabancin PDP na kasa har sau hudu domin gabatar da korafinsu, da kuma kokari warware matsalar.

Har yanzu ba a kai ga bayyana 'yan kwamitin ba, sai dai wasu kafofin yada labaran Najeriya sun ruwaito cewa makusantan Kwankwaso za a nada.

A ranar Asabar din da ta gabata ne uwar jam'iyyar PDP ta kasa ta bayar da sanarwar rushe shugabancin jam'iyyar na Kano, sai dai har yanzu ba a ba da dalilan daukar matakin ba.

Sanarwar da mai magana da yawun jam'iyyar ya fitar ta ce za a maye gurbin shugabannin da aka rushe da kwamitin rikon kwarya.

Har yanzu ba a kai ga bayyana 'yan kwamitin ba, sai dai wasu kafofin watsa labaran Najeriya sun rawaito cewa makusantan Kwankwaso za a nada.

Kawo yanzu dai Malam Shekarau bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba shi da magoya bayansa.

Sai dai wasu bayanai na cewa akwai alama zai koma jam'iyyar APC ne, wacce a baya ya fice bayan shigar Kwankwaso.

A shekarar 2015 ne Malam Shekarau ya fice daga APC bayan zargin shugabancin jam'iyyar na lokacin da nuna musu rashin adalci ta hanyar fifita bangaren Kwankwaso a kansu.