Syria: Trump ya ce za a yi babban kuskure a Idlib

'Yan tawaye a Idlib na shiryawa harin da dakarun gwamnati za su kai yankin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan tawaye a Idlib na shiryawa harin da dakarun gwamnati za su kai yankin

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Shugaban Syria Bashar al-Assad bisa kai hari yankin Idlib da 'yan tawaye ke rike da shi a Syriar, inda ya ce dubban mutane ka iya mutuwa idan a ka kai harin.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mr Trump ya ce idan har Rasha da Iran su ka taimakawa Syria wajen kai farmakin, lallai zai zama sun yi kuskure mai girman gaske.

Ya kuma ce ganganci ne kai hari a yankin Idlib saboda dubban fararen hula na iya mutuwa a harin. Itama Majalisar Dinkin Duniya ta ce kai hari Idlib ka iya zama babban bala'i ga dubban fararen hula a yankin.

Bayanin Mr Trump ya zo a daidai lokacin da gwamnatin Syria ke shirin kai wani babban farmaki a yankin na Idlib, wanda ke hannun kungiyoyin mayakan sa kai da yawa, wadanda a ka koro daga wasu sassa daban-daban na kasar.

An tura dubban dakaru yankin don korar 'yan tawayen da a ka yi kiyasin sun kai dubu talatin.

A sama da shekara bakwai na yakin a Syria, sama da mutane 400,000 su ka mutu yayin da wasu kuma sun bata.