Habibu Sani Babura: Malamin da bai san nakasa ba

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa

Ashe mutuwa tai min gaggawa, ta dauke Ciroman Gombe

Allah jikan Ciroman Gombe

- Marigayi Alhaji Mamman Shata, a cikin wakar Ciroman Gombe

Asalin hoton, NO CREDIT

Na taba jin wannan wakar a bakin Dokta Habibu Sani Babura, wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar Talata a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

Baba Habibu, kamar yadda aka fi sanin sa a Jami'ar Bayero ta Kano, inda ya shafe fiye da shekara 30 yana koyarwa, mutum ne na kowa.

Ya yi fice a fannoni da dama na ilimi amma babban abin da za a fi tuna shi akai shi ne sha'awarsa ta bunkasa harshen Hausa da taskace al'adun Hausawa.

Wani abin mamaki da sha'awa a game da rayuwarsa shi ne rashin nuna gazawa a kan aikinsa duk kuwa da cewa yana da nakasa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Malam Habibu Sani Babura ya yi hatsarin mota a shekarun 1980 lamarin da ya sa dukkan jikinsa ya shanye, don haka duk gwagwarmayar da ya yi ta rayuwa, ya yi ta ne a kan keken guragu.

Wannan taliki ya ja hankalina ne a shekarar 2000 lokacin ina ajin farko na karatun digiri a harshen Hausa.

A watan Maris na shekarar, lokacin da nake kan hanyata ta hawa benen da Sashen Nazarin Harsunan Najeriya yake a Sabon Matsugunin Jami'ar Bayero, sai na ga ana kokarin hauro da wani mutum sama, da a wancan lokacin ban san ko wane ne ba, bisa keken guragu.

Na yi tsammani dalibi ne amma da na zura ido sosai sai na ga dattijo ne kuma yana magana radau kamar bai damu da kokarin da ake na hawa da shi benen ba.

A lokacin ne na tambayi abokaina Ali Wada Muhammad (Hydar) da Ahmed Salisu, wadanda ajinmu guda da su, ko wane ne wancan mutumin - suka ce sunansa Dokta Habibu Sani Babura kuma Malami ne da ke koyar da harshen Hausa.

Amma ban soma mayar da hankali sosai kan Baba Habibu ba sai lokacin da muka yi kicibis da shi a hanyar ginin da Tsangayar koyar da Ilimin Manya (Adult Education) take.

A lokacin ina tare da Halima Hafiz Ringim, diyar tsohon babban sufeton 'yan sandan Najeriya, Hafiz Ringim, wadda ita ma ajinmu guda.

Yadda na ga ta tsuguna ta gaishe shi da kuma yadda suka rika raha ya ba ni sha'awa matuka.

Baba Habibu zai iya sanya mutum ya yi dariya har cikinsa ya yi ciwo.

Daga bisani Halima ta gaya min alakar da ke tsakaninsu - ta ce abokin mahaifinta ne kuma shi ne ya taimaka mata ta samu gurbin karatu a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya.

Ban tashi sanin irin baiwar da Allah ya yi wa Baba Habibu ba sai a shekara ta 2003 lokacin da ya koyar da mu wani kwas mai suna Introductory Socio-linguistics.

Wannan kwas, yana magana ne kan ire-iren hausar da wasu rukunin jama'a ke yi. Misali, da mutum ya ji ana cewa 'Baabaa, zan ware (wato zan tafi), mu bace (mu tafi), to ya san Hausar 'yan daba ce.

Ko kuma ka ji ana cewa 'Ma Sha Allah, wato ainifin (wato ainihin) da sauransu, ka san hausar Ustazai ce.

'Ba nakasasshe sai kasasshe'

Asalin hoton, NO CREDIT

Bayanan hoto,

Nakasar da ta samu marigayi Dokta Babura ba ta hana shi komai ba

Malam Habibu Sani Babura ya yi amfani da hazakarsa wurin koyar da wannan kwas ta yadda ban so ya fita daga ajinmu ba lokacin da ya zo rufe kwas din a karshen zangon karatu.

Hasalima, na ga 'yan ajinmu da dama da suka zub da kwalla lokacin da yake yi mana nasiha - ya ce watakila ba za mu sake haduwa ba har abada, don haka yana neman gafarar duk dalibin da ya taba wa rai.

A lokacin ne na ji ya rera wakar da Mamman Shata ya yi ta rasuwar Ciroman Gombe

Abin takaicin shi ne, ban sake sanya shi a idanuna ba tun ranar da ya yi waccan maganar har rai ya yi halinsa.

Babban darasin da mutane za su koya game da rayuwar Dokta Habibu Sani Babura shi ne yadda nakasa ba ta hana shi jajircewa ya nemi na kansa ba.

Babu wani bangare na jikin marigayin da ke aiki idan ban da kansa inda yake magana tamkar kowanne mai cikakkiyar lafiya.

Samun mutum kamar Baba Habibu a arewacin Najeriya, inda 'yar karamar nakasa kan sa mutane su koma mabarata, ba karamin abin alfahari ba ne.

Allah Ya jikan Dokta Habibu Sani Babura, Ya sa bakin wahala ke nan. Mu kuma Allah Ya ba mu hakurin wannan babban rashi.