NFF ta dakatar da kocin Najeriya Salisu Yusuf bisa karbar 'cin hanci'

Kocin Super Eagles Salisu Yusuf
Image caption Salisu Yusuf ya ce kudin da ya karba ba su saba wa ka'ida ba

Hukumar kula da kwallon kafar Najeriya, NFF, ta dakatar da mai horas da 'yan wasan Super Eagles Salisu Yusuf tsawon shekara daya bayan ta same shi da laifin karbar cin hanci.

Wata sanarwa da mai magana da yawun NFF, Demola Olajire, ya fitar ranar Laraba ta ce an dauki mataki ne bayan sun karbi rahoton kwamitin kula da da'a na hukumar, wanda ya bincika sanna ya gano cewa Salisu Yusuf ya karbi na-goro.

Wani hoton bidiyo da shirin BBC Africa Eye ma hallasa jama'a ya nada a asirce ya nuna yadda mai horas da 'yan wasan Super Eagles ya karbi kudi a hannun wasu mutane yayin tattaunawa kan zaben 'yan wasan da za su taka rawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Mutanen sun ba wa kociyan kudi ne yayin da suka nuna masa tamkar wakilai ne na wasu 'yan wasa da ke son a dauke su domin taka rawa a gasar CHAN ta masu taka-leda a cikin gida.

Sai dai Salisu Yusuf, ya shaida wa BBC cewa ba ya tunanin ya karya dokokin hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, wadda ta haramta wa jami'anta karbar na-goro.

'Yan jaridar na BBC sun yi aiki ne tare da Anas Armaya'u, wani dan jarida mai binciken kwa-kwaf na kasar Ghana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba Salisu Yusuf kadai ne dan Najeriya da aka taba dakatarwa a harkar kwallon kafa sabida cin hanci da rashawa ba

'Abin da kwamitin da'a ya gano'

NFF ta bukaci kociyan ya biya tarar $5,000 nan da wata uku masu zuwa.

Rahoton kwamitin da'ar, wanda tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu ya gabatar bayan ya gana da kociyan domin sauraren nasa bangaren, ya gano ceewa lallai kociyan ya karbi hancin $1,000 da wata kungiyar da ya yi ikirarin kula da 'yan wasa ta Tigers Player's Agency, ta ba shi a madadin 'yan wasa Osas Okoro da Rabiu Ali, saboda sanya su a cikin tawagar da ta shiga gasar CHAN ta 2018 da aka yi a Morocco.

Babu tabbas ko kudin da kocin ya karba ya yi tasiri a kansa wajen zabar 'yan wasan.

Tun farko Salisu Yusuf, sai da ya shaida wa 'yan jaridar cewa zabar yan wasan da za su buga a gasar CHAN ana yi ne dangane da kokarin mutum da kuma kasancewar yana buga wasa a koda yaushe.

Sannan kuma ya shaidawa BBC cewa shi dala 750 ya karba, ba dala dubu guda ba, kuma ya yi amanna cewa kudin ba su yadda haramcin karbar na goron FIFA zai shafe shi ba.

Kawo yanzu babu wani martani da ya fito daga Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF, wacce ta samu kanta a cikin wani rikici na shugabanci.