Hotunan yadda aka gudanar da bikin dasa itatuwa a Nijar

Nijar
Bayanan hoto,

Uwar gidan shugaban kasar Nijar a lokacin da take kaddamar da wani tsari na dashen itatuwa 30,000

An kaddamar da wani tsari na dashen itatuwa 30,000 da mai dakin shugaban kasar Nijar ta jagoranta a ranar Litinin.

Makasudin wannan shiri in ji wadanda suka shirya shi ne na kayata birnin Yamai, baya ga yaki da kwararowar hamada.

Itatuwan gargajiya irin su dinya, taura da sauransu ne dai ake dasawa, wanda hakan zai ba matasa damar sanin itatuwan da ke neman bacewa.

Bayanan hoto,

Uwargidan Shugaban Nijar ce Lalla Malika Issoufou ta jagoranci bikin a ranar Litinin

Bayanan hoto,

Dasa itatuwan za su ba wa matasa damar sanin itatuwan da ke neman bacewa

Bayanan hoto,

Manyan baki daga sassa daban-daban sun halarci biki