Najeriya ta 'kakaba' wa MTN harajin biliyan 612

MTN

Asalin hoton, Reuters

Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka, MTN, ya ce Najeriya ta "kakaba" masa harajin dala biliyan biyu (Naira biliyan 612), 'yan kwanaki bayan Babban Bankin Kasar ya ci kamfanin tarar dala biliyan 8 (wato kimanin naira triliyan 2.4).

Saboda matsalolin da MTN ke fuskanta a harkar sadarwa da ke kawo makudan kudi, hannayen jarin kamfanin sun fadi da kashi 20 cikin 100 cikin mako guda.

MTN ya ce ofishin ministan shari'a na kasar ya yi lissafin cewa ana bin kamfanin bashin dala biliyan biyu (naira biliyan 612) na harajin shigo da kayayyaki, da kuma biyan kudi ga 'yan kwangila cikin shekaru 10 da suka wuce.

Kamfanin ya musanta adadin kuma ya ce shi ya riga ya biya dala miliyan 700 (Naira bliyan 214).

Bayannin harajin a kan MTN ya fito ne a cikin wata sanarwar da ta yi karin bayani game da dala biliyan 8.1 da babban bankin Najeriya ya ce an fitar daga kasar ba bisa ka'ida ba.

Babban bankin ya ce idan MTN ya mayar da kudin da ya fitar kasar, za a mayar wa kamfanin kudin da takardar kudin kasar, Naira.

A shekarar 2015 hukumar kula da harkar sadarwar Najeriya ta ci tarar kamfanin na kasar Afirka ta Kudu dala biliyan biyar don kin bin umarnin gwamnati na katse layukan mutum miliyan biyar da ba a yi musu rijista ba.

Daga baya an rage tarar zuwa dala bliyan 1.7.

Fiye da 'yan Najeriya miliyan 50 ne ke amfani da MTN, kuma kaso 30 cikin dari na harkar cinikayyar kamfanin na gudana ne a kasar.