An daina gyaran na'urar wasan kwamputa ta PlayStation a Japan

Asalin hoton, Getty Images
Na'urar PlayStation 2 ce aka fi saya a duniya.
Kamfanin Sony ya daina gyaran na'urar wasan kwamputa ta PlayStation 2 shekara 18 bayan an fara sayar da ita.
An soma sayar da na'urar wasan ne a Japan a watan Maris din 2000, kuma tun daga nan babu wata na'urar wasan kwamputa da aka taba sayarwa kamar yadda aka saye ta.
An daina kera na'urar ne a 2012, shekara shida bayan an fitar da na'urar da ta fi ta, wato PlayStation 3 (PS3).
Kamfanin Sony ya ce ba zai iya gyaran ta ba, kuma kayan gyaran tsohuwar na'urar sun kare.
A cikin wata sanarwa, kamfanin ya gode wa abokan huldarsa saboda yadda suka ci gaba da nuna sha'awarsu kan wasan.
Masu neman a gyara musu na'urar da ta lalace a yanzu sai dai su kai wajen masu gyara-samun-sa'a.
An sayar da sama da na'urar wasan na kwamputa ta PlayStation 2 sama da miliyan 150.
Samfurin da ake amfani da ita a yanzu kuwa wato PS4 an sayar da kimanin guda miliyan 80.