An tilastawa dalibai mata kwana a cikin tsananin sanyi

Asalin hoton, NationBreakingNews
An sa yaran sun kwana a sanyi ne saboda ba su ci jarrabawa ba.
An fusata iyayen dalibai a Kenya bayan tilastawa 'yan mata sama da 30 kwana a tsakiyar wani fili cikin tsananin sanyi a wata makarantar kwana.
'Yan matan da ke karatu a sakandaren Nasokol a garin Pokot da ke yammacin kasar, sun zargi shugabar makarantar da daukan wannan hukunci saboda rashin kokari a jarrabawa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A baya wani shirin bada tallafi a harkar tamaula ya taba jan hankali akan tsadar kudin makarantar, da kuma rashin samun biyan bukata la'akari da kokarin daliban, a cewar jaridar Daily Nation ta kasar.
Sai dai sabuwar shugabar makarantar ta yanzu ta bijiro da na ta tsarin da nufin inganta sakamakon jarabawar dalibai mata da kuma soke duk wasu tsare-tsare da ta gada daga magabanciyarta.
Yanzu kusan 'yan mata da shekarunsu ke tsakanin goma sha biyar zuwa goma sha bakwai aka kora daga makaranta a yammacin ranar litinin saboda dalilai na rashin tabuka abin a zo a gani a jarabawa.