Ko PDP za ta iya sulhunta 'ya'yanta a Kano?

PDP

Asalin hoton, PDP

Bayanan hoto,

PDP ta ce tana kokarin tafiya da kowa a Kano

Kwamitin koli na jam'iyyar PDP a Najeriya ya fadada kwamitin rikon shugabancin jihar, domin tafiya da duka bangarorin jam'iyyar.

Jam'iyyar ta kuma ce a shirye take ta saurari dukkan ra'ayoyi da shawarwarin 'ya'yanta, domin tabbatar da masalaha, da kuma lura da bukatun manyan jagororin jam'iyyar a jihar.

Wata sanarwa da kakakin PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce a shirye jam'iyyar take ta tattauna da jagororin jam'iyyar da suka fusata.

Ta kara da cewa za ta tabbatar an janye karar da shugabannin jam'iyyar na jihar (da aka rushe) suka shigar gaban kotu suna kalubalantar jam'iyyar a matakin kasa.

Sanarwar na zuwa ne bayan tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam'iyyar saboda zargin rashin adalci wajen rabon mukamai, inda bangarensa ya yi zargin cewa za a ba wa bangaren Sanata Rabi'u Kwankwaso 51% na shugabancin jam'iyyar, yayin da sauran bangarori kuma za su dauki 49%.

Har yanzu PDP a hukumance ba ta bayyana kafa kwamitin rikon jam'iyyar a Kano ba, wanda wannan ne zai tabbatar da inda jam'iyyar ta karkata.

A ranar Talata ne uwar jam'iyyar ta PDP ta sanar da rushe shugabanninta a Kano, amma ba ta bayyana dalilan rushewar ba.

Mun yi yunkurin jin ta bakin bangaren Shekarau kan matakin na PDP na baya-bayan nan, sai dai duka wadanda muka tuntuba wayoyinsu na kashe.