Siyasar Kano: Muna maraba da matakin PDP – Kwankwasiyya

Kwankwaso da Shekarau

Asalin hoton, @KwankwasoRM

Bayanan hoto,

PDP ta ce Shekarau ya dade yana son komawa APC

Al'amuran siyasar a jihar Kano sun dauki wani sabon salo a farkon watan Satumabar da muke ciki bayan uwar jam'iyyar PDP ta kasa ta bada sanarwar rushe shugabancin jam'iyyar jihar.

Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce za a nada kwamitin rikon jam'iyyar, to sai dai har kawo yanzu ba a bayyana nadin kwamitin rikon ba, da kuma wadanda za su jagoranci jam'iyyar.

Matakin dai ya zo wa wasu mutane ba-zata, domin babu wani laifi da aka tuhumi zababbun shugabannin da aikatawa, kuma babu wani da ya ke kalubalantar shugabancinsu.

To sai dai a iya cewa manyan jam'iyyar suna da masaniyar cewa hakan za ta iya faruwa, kuma ma sun ga alamun hakan, tun bayan shigar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso PDP, bayan sauya sheka daga APC.

Tsofaffin 'yan jam'iyyar musamman bangaren tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau sun yi watsi da matakin, inda suka bayyana cewa hakan tsagwaron rashin adalci ne.

Bangaren tsohon gwamna Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso murna suka yi da matakin, suka kuma karbe shi hannu, biyu-biyu, saboda za a ba su wani bangare na shugabancin jam'iyyar.

Wani babban na hannun daman Kwankwaso Kwamared Aminu Abdussalam ya shaidawa BBC cewa, bai kamata wasu 'yan jam'iyyar su nuna rashin gwamsuwa da matakin rusa shugabannin ba, a cewarsa kamata ya yi su mika wuya, su kuma amince da duk abinda zai biyo baya.

Rabon shugabancin PDP a Kano

Bayanai daga majiyoyi daban-saban sun nuna cewa an fara kai ruwa rana tsakanin jagororin PDP a Kano jim kadan bayan shigar Kwankwaso jam'iyyar a watan Yuli.

Takaddamar ta taso ne kan yadda za a mikawa bangaren Kwankwasiyya mafi yawan shugabannin jam'iyyar, in ya so sauran shugabanni kuma su raba abin da ya rage tsakaninsu, matakin da su Shekarau suke gani tamkar yi musu kora da hali ne.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wani makusancin Shekarau ya ce sau hudu ana zama a Abuja domin a shawo kan matsalar rabon shugbancin, amma lamarin ya ci tura.

Duka bangarorin Kwankwaso da na Shekarau sun tabbatar da cewa abin da ya janyo sabani shi ne alkawarin da uwar jam'iyyar ta kasa ta yi wa Kwankwaso cewa za a ba shi kashi 51% na shugabacin jam'iyyar, ciki har da shugaba.

Bangaren su Shekarau da sauran shugabannin jam'iyyar dai sun ce hakan rashin adalci ne tsagwaronsa, hakan ce ma ta sa wasu dubban 'yan jam'iyyar suka yi wata zanga-zangar adawa da matakin ranar Litinin.

Su kuma a bangaren 'yan Kwankwasiyya sun ce hakan shi ne daidai, domin Kwankwaso ya shiga PDP da wasu 'yan majalisa.

Kwamared Aminu Abdussalam ya ce "rashin fahimta ne ya sa wasu ke adawa da matakin da uwar jam'iyyar ta kasa ta dauka," in ji shi.

"Kwankwaso ya kawo wa PDP a Kano sanata, da 'yan majalisar wakilai tara, da 'yan majalisar dokoki ta jiha bakwai, da kuma dimbin magoya baya" A cewar Kwamared.

Don haka ne ya ce ya kamata kowa ya zo ya hada kai da Kwankwaso domin kai jam'iyyar gaci.