'China ta tsare musulmi yan Uighurs miliyan daya'

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu da rahotannin tsare dubban musulmai yan kabila Uighurs a China, kuma ta yi kira a saki mutanen da aka tsare, da sunan yaki da ta'addanci.

Matakin ya zo ne bayan wani kwamitin majalisar ya bada rahoton cewa ana tsare da musulmi 'yan kabilara ta Uighurs sama da miliyan daya a wasu sansanoni da sunan sauya musu halayya a garin Xinjiang da ke yammacin kasar.

Yana kabilar ta Uighurs su ne 40% na mazauna yankin. Sai dai hukumomin China sun musanta zargin.