Har yanzu ina nan a PDP — Shekarau

Malam Ibrahim Shekarau

Asalin hoton, Ibrahim Shekarau/Facebook

Bayanan hoto,

Shekarau ya ce shi zai yi bayani da kansa kan matakin da ya dauka bayan ya gama tattaunawa da jama'arsa.

Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce har yanzu yana cikin jam'iyyar PDP.

A wani sakon murya da ya fitar, Malam Shekarau ya ce har yanzu suna tattaunawa da sauran jagororin jam'iyyar na Kano kan matakin da ya kamata su dauka, sakamakon rushe shugabancin jam'iyyar a jihar.

A wannan makon ne mai magana da yawun tsohon gwamnan Malam Sule Yau Sule ya shaida wa BBC cewa Shekarau da magoya bayansa sun fice daga PDP, saboda zargin rashin adalci.

Sai dai daga baya Sule Ya'u ya ce an yi wa maganar ta sa mummunar fahimta.

A sakon muryar, wanda Shekarau ya aike wa magoya bayansa, ya ce ba zai dauki wani mataki ba sai ya tattauna da abokan tafiyarsa a siyasa.

Ya jadda cewa ba su amince da matakin PDP na rushe shugabancin jam'iyyar ba na rushe shugabancin na Kano ba gaira ba dalili, wanda hakan ya ce ya sabawa kundin tsarin mulkin PDP.

Malam Shekaru ya ce da kansa zai yi wa magoya bayansa bayani kan irin matakin da ya dauka idan lokaci ya yi.

A nasu bangaren, magoya bayan Sanata Rabiu Kwankwaso sun ce sun yi marhabin da matakin PDP din.

A karshen watan Yuli ne Sanata Kwankwaso da wasu 'yan majalisu suka koma PDP bayan ficewa daga APC.

A ranar Talata jam'iyyar PDP ta fitar da wata sanarwa inda ta ce ta fadada kwamitin rikon jam'iyyar na Kano, ta yadda za a tafi da kowa.

Ta kuma kara da cewa tana tuntuba tare da tattaunawa da 'ya'yanta da wannan lamari ya shafa, inda kuma take maraba da duk wata shawara ko ra'ayi da za su kawo hadin kai a jam'iyyar.