An ceto daruruwan 'yan Afirka a saharar Nijar

Niger

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Da dama daga mutanen sun karasa garin Assamaka da kafa a yunkurinsu na tsallakawa Nahiyar Turai.

Kungiyar kula da masu kaura ta duniya ta ce an ceto fiye da 'yan Afirka ta yamma 400 da suke a saharar jamhuriyar Nijar.

Kamfanin dillacin labarai Reuters ya ambato kungiyar tana cewa jami'anta masu bincike ne suka gano mutanen a cikin sahara, a garin Assamaka da ke kan iyaka.

An gano mutum 347 a tawaga ta farko, wandanda sun karasa garin ne da kafa ranar Litinin.

Kuma mutanen sun fito ne daga kasashe 13 da suka hada da Mali da Guinea da Senegal.

Sauran 92 kuma an gano su ne ranar Talata, kamar yadda Reuters ya ruwaito daga kungiyar.

Nijar dai wata madakata ce ga duban 'yan ci-rani da ke tafiya Libiya ko Algeriya, inda daga nan kuma suke yunkurin tsallaka takun Bahar Rum domin shiga nahiyar Turai.

Bayanan hoto,

Garin Assamaka