Su wa suka saya wa Buhari fom din takara?

NCAN

Asalin hoton, NCAN

Bayanan hoto,

Matasa ne suka sayawa Buhari fom din Naira miliyan 45

Wasu matasan Najeriya sun saya wa shugaban kasar Muhmmadu Buhari fom din takara a kan Naira miliyan 45.

Matasan na kungiyar Nigeria Ambassadors Consolidation Network sun saya wa shugaban fom din ne jim kadan bayan jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta fitar da kudaden da masu neman takara a jam'iyyar za su sayi fom.

Fom din shugaban kasa ne ya fi kowanne tsada, da ake sayar da shi a kan Naira miliyan 45.

To sai dai abin da mutane da dama ke mamaki shi ne yadda matasan suka sami miliyoyin kudin da suka saya wa Buhari fom din.

Bugu da kari hakan ya faru ne a daidai lokacin da wasu 'yan uwansu matasa ke korafin cewa kudin da jam'iyyar ta sanya ya yi musu tsada.

Akwai masu ra'ayin cewa matasan na rawa ne da bazar wasu manyan 'yan siyasa da suka ba su kudin sayen fom din, don a nuna cewa har yanzu Buhari yana da farin jini a wajen matasan kasar.

To sai dai shugaban kungiyar ta Nigeria Ambassadors Consolidation Network Barista Sanusi Musa ya ce ko kadan ba bu wani jami'in gwamnati da ya basu kudi.

"Bari in yi rantsuwa, Wallahi tallahi babu wani jami'in gwamnati da ya ba da ko kwabo a kudin da muka biya," in ji Sanusi Musa.

Ya kara da cewa, matasan sun kai shekara guda suna tara kudi domin saya wa shugaban fom.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana ta ce-ce-ku-ce a kan fom din naira miliyan 45 da matasan suka saya wa Shugaba Buhari

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Mutum daya ne, wani dan kasuwa dan kabilar Ibo kadai ya kawo mana gudunmuwar Naira miliyan biyar, da ya ji abin da muke shirin yi," in ji shi.

A cewarsa sun gamsu da irin shugabancin Buhari, don haka ne suka yanke hukuncin mara masa baya a zaben da ke tafe.

A zaben shekarar 2015 ma Muhammadu Buhari ya samu gudunmuwa daga 'yan kasar da dama wajen saya masa fom din takara da kuma kudin yakin neman zabe.

Sai dai wasu suna ganin da wuya a wannan karon ya samu irin wannan gudunmawar, kasancewar wasu 'yan kasar sun dawo daga rakiyarsa.

Wannan tunanin da wasu 'yan kasar ke yi na daga dalilan da Sanusi Musa ya bayyana cewa suka saya wa Buhari fom din, domin nuna wa jama'a cewa har yanzu matasa suna goyon bayan Buhari.

A shekarar 2014 dai kwamitin yakin neman zaben Shugaba Buhari ya fitar da wani kati wanda jama'a za su iya amfani da shi wajen ba wa Buhari gudunmuwa.

To sai dai babu tabbas ko a wannan karon ma za a yi amfani da wannan hanyar.

Kuma idan ma za a yi din shin jama'a za su bayar da gudunmuwa irin yadda suka bayar a baya?

Asalin hoton, NCAN

Bayanan hoto,

Matasan sun ce sun gamsu da mulki Buhari.