Trump ya karyata littafin Woodward kan Assad

Trump ya ce bayanan karya ne a littafin Woodward

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Trump ya ce bayanan karya ne a littafin Woodward

Sabon Littafin da aka wallafa game da shugaban Amurka Donald Trump ya ce shugaban sakarai ne kuma makaryaci.

Shugaba Trump ya yi watsi da littafin wanda kuma ya yi ikirarin cewar ya bai wa ma'aikatar tsaron Pentagon umarnin kitsa yadda za a kashe shugaba Bashar al Assad na Syria.

Tsohon dan jarida Bob Woodward wanda ya rubuta littafin ya ce sakataren tsaron Amurka James Mattis ne ya fada ma shi cewar Mista Trump ya bukaci hakan bayan wani harin makami mai guba da Syria ta kai

Littafin mai suna "Fear: Trump in the White House," a turance, wanda jaridar Washington Post ta wallafa a ranar talata, wani sabon rikici ne da ya sake kunno kai a Fadar White House karkashin mulkin Trump na watanni 20.

Littafin ya bayyan Trump a matsayin mutum da ke da rauni kuma wanda baya tunani wajen daukar mataki da kuma yanke hukunci.

Littafin wanda ya bayyana rikicin da ke tattare a gwamnatin Trump, ya kuma bayyana yadda manyan jami'an gwamnatii ke boye wasu muhimman bayanai ga shugaban.

Bayanan da ke kunshe a littafin kuma sun ce shugaba, Trump ya bukaci a halaka shugaban Syria a bara amma sakararen tsaron Amurka James Mattis ya yi watsi da bukatar.

Mawallafin littafin ya ce sakararen tsaron Amurka ne ya shaida masa cewa shugaba Trump ya bayar da umurnin, bayan harin makamai mai guba da aka kai a watan Afrilun 2017.

Amma a wasu jerin sakwanni a Twitter, Mista Trump ya karyata dukkanin bayanan da ke cikin littafin wanda ya danganta a matsayin yaudara kuma abin da ya kamata jama'a su kyamata.

Shi kansa Mista Mattis sakataren tsareon Amurka ya nesanta kan shi da littafin tare da karyata ikirarin marubinsa kan bayanan da ya ce ya same su daga gare shi.

A ranar 11 ga watan satumba ne za a saki littafin.