Abin da ya sa fom din mu ya yi tsada — APC

Asalin hoton, Getty Images
Wasu na ganin kudin da APC za ta sayar da fom ya yi matukar yawa
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi karin bayani kan dalilin da ya sa ta sanya kudi mai yawa domin sayen fom din neman takara a cikinta.
Jam'iyyar ta ce wannan ce hanyar da za ta samu kudin da za ta yi hidimomin da ke gabanta a 'yan kwanakin da ke tafe.
Ranar Laraba ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta soma sayar da fom ga masu son yin takara a inuwarta a zaben 2019.
Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar kan tsarin sayar da fom da gudanar da tarukan tsayar da 'yan takara ranar ta Laraba, ta ce za a soma sayar da fom ne sannan a kammala da taron zaben wanda zai yi mata takarar shugabancin kasa a ranar Asabar, shida ga watan Oktoba na 2019.
Sai dai babban abin da ya fi jan hankulan 'yan jam'iyyar da ma 'yan kasar baki daya shi ne tsawwalawar da APC ta yi kan kudin sayar da fom din neman takara.
Wani dan jam'iyyar da ke son tsayawa takarar majalisar dokokin tarayya a jihar Kano, Surajo Sani Marshall, ya shaida wa BBC cewa tun da ya soma harkokin siyasa bai taba ganin jam'iyyar da ta tsuga kudin sayen fom kamar APC ba.
"Ta yaya APC za ta sayar da fom din takarar majalisar dokokin tarayya kan N3,850,000 sannan ta ce ita jam'iyyar talakawa ce?," in ji Surajo Marshall.
Kudin sayar da fom:
- Takarar majalisar jiha - N850,000
- Takarar majalisar dokokin tarayya - N3,850,000
- Takarar majalisar dattawa - N7,000, 000
- Takarar gwamna - N22,500,000
- Takarar shugaban kasa - N45,000,000
Asalin hoton, Getty Images
Wasu na ganin kudin da APC za ta sayar da fom ya yi matukar yawa
Sakataren jam'iyyar ta APC na kasa Malam Mai Mala Buni ya bayyanawa BBC cewa jam'iyyar ta yi la'akari ne da bukatun da ke gabanta na kudi kafin yanke kudaden.
Ya ce da kudaden fom din da aka saya ne APC za ta yi amfani wajen shirya wa da gudanar da zabukan fitar da gwani a duka fadin kasar.
Mai Mala ya ce da kudaden ne za a yi amfani wajen biyan jami'an da za su saka ido kan zabukan fitar da gwani, da kuma sayen duka kayayyakin zabe da buga wadanda za a buga.
Ya ce, kudin bai yi yawa ba, idan aka yi la'akari da cewa da jam'iyyar ba ta diban kudin gwamnati wajen gudanar da al'amuranta.
Tuni dai wata kungiyar matasan kasar ta saya wa Shugaba Buhari fom din neman tsaya wa takarar shugaban kasa a kan kudi Naira miliyan 45.