Facebook da Twitter sun sha tsauraran tambayoyi kan zabe

Asalin hoton, AFP
Jack Dorsey da Sheryl Sandberg sun isa birnin Washington DC kusan lokaci guda
'Yan majalisar dokokin Amurka sun yi wa shugabannin shafukan sada zumunta da muhawara na Facebook da Twitter tambayoyi kan yadda za su kauce wa tsoma baki a zabukan kasar da ke tafe.
Babbar jami'ar Facebook Sheryl Sandberg ce ta wakilci kamfanin, yayin da shugaban Twitter Jack Dorsey ya wakilci nasa kamfanin.
Google bai tura wakili ba, kamar yadda aka yi tsammani.
A lokacin da yake bude taron jin bahasin jama'a, dan majalisar daddatwa na jam'iyyar Democrat Mark Warner ya ce ya "matukar rashin jin dadi" saboda kin zuwan da jami'an Google suka yi da kuma rashin aika wakili.
Kwamitin na majalisar dattawa ya mayar da hankali ne kan matakan da kafofin sada zumuntar ke amfani da su wurin ganin ba su bari wani ya yi tasiri a zabukan da za a yi nan gaba ba.
Ana zaman sauraren bahasin ne bayan zargin da aka yi cewa kasar Rasha da wasu 'yan-koren ta sun yada labaran karya da farfaganda gabanin zaben shugaban Amurka na 2016.
"Idan muka yi la'akari da abubuwan da suka faru a baya, za mu gano karara cewa Facebook da Twitter sun tafka kuskure. Ku, kamar gwamnatin Amurka, kun fadi ba nauyi game da harin da aka kai kan tsarin zabenmu. Ko da bayan zaben, kun yi kasa a gwiwa wurin amincewa an samu matsala," in ji Mr Warner.
Ya yi gargadin cewa kamfanonin sada zumuntar ka iya fuskantar sabbin dokoki na sanya ido.
Mr Warner ya kara da cewa lokacin da za a bar shafukan sada zumunta su ci karensu babu babbaka a kasar ya wuce.
Gabanin sauraren bahasin, Facebook ya mika shaidunsa a rubuce inda ya yi bayani kan yadda ya hana shafukan bogi 1.27 bn sakat tsakanin watan Oktoban 2017 zuwa watan Maris na 2018.
Ya kara da cewa ya dauki mutum 20,000 domin sanya ido sosai kan yadda ake mu'amala a shafin.
Shi ma shugaban Twitter Mr Dorsey ya mika nasa shaidun gabanin zaman bahasin, inda ya musanta zargin amfani da shi wurin yada labaran kanzon-kurege.
Asalin hoton, Reuters
Shugaba Twitter Jack Dorsey