Dakatar da kocin Najeriya sabon babin yaki da rashawa ne - Ribadu

Malam Nuhu Ribadu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rabadu ya ce dole doka ta hau kan kowa

Tsohon shugaban hukumar EFCC da ke yaki da rashawa a Najeriya Malam Nuhu Rabadu ya ce sun bude sabon babin yaki da cin hanici da rashawa a kasar bayan dakatar da kocin tawagar kwallon kafar kasar, Salisu Yusuf.

Malam Nuhu Ribadu, wanda shi ne shugaban kwamitin da'a da tabbatar da gaskiya da adalci, na hukumar kwallon kafar Najeriya, ya kuma ce a yadda kasar ke tafiya dole kowa ya kawo na shi taimako.

Kwamitin ne ya yi nazari kan zargin da aka yi wa Salisu Yusuf na karbar kudi a wani bidiyo tare da dakatar da shi na tsawon shekara guda da kuma cin sa tarar dala dubu biyar.

Matakin ya biyo bayan ganin Kocin a bidiyo yana karbar kyautar kudi daga wasu manema labaru da suka yi shigar burtu suna neman a yi wa wasu 'yan wasa alfarmar saka su a wasa.

Malam Ribadu ya shaida wa BBC cewa al'amarin ya janyo wa Najeriya bacin suna kwarai, kuma an zura ido a ga matakin da kasar za ta dauka.

"An nuna wa duniya cewa kocin Najeriya ya karbi kudi, kowa ya gani a bidiyo," in ji shi.

Ya ce dokar NFF ta haramta wa mutum karbar kudi, a kowane yanayi, ko na kyauta ne.

Ya ce duk wanda aka kama ya karbi kudi bayan an haramta, to dole hukunci ya hau kan mutum.