An samu sojoji da laifin yi wa mata masu aikin agaji fyade

South Sudanese soldiers stand during their sentencing over the rape of foreign aid workers and the murder of a local journalist in an assault on the Terrain Hotel in the capital Juba in 2016 at a military court Juba, South Sudan, September 6, 2018.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan dai lamari ne da ba a cika ganinsa ba inda aka sami sojoji da laifin cin zarafin mutane

Wata kotun soji a Sudan Ta Kudu ta samu sojoji 10 da laifin yi wa ma'aikatan agaji fyade tare da kashe wani dan jarida.

Kotun ta kuma umarci gwamnatin Sudan ta Kudu ta biya kowa cikin wadanda aka yi wa fyaden dala dubu 4 (naira miliyan 1.2) a matsayin diyya.

An aikata laifukan ne a lokacin da aka kai samame otel din Terrain Hotel a babban birnin kasar, Juba a shekarar 2016.

An zargi sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kusa da kasa kai dauki a lokacin da ake neman taimakonsu.

An gabatar da hukuncin ne a wata kotun soji makere da jami'an diflomasiyya da kuma ma'aikatan ba da agaji.

An wanke wani soja daga aikata laifi yayin da wani soja kuma ya mutu.

An kaddamar da harin ne a yayin da ake fafatawa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a Juba.

An kashe sama da mutum 70, ciki har da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Kotun ta bai wa gwamnati umarnin biyan dan Birtaniya mai oten din, Mike Woodward, dala miliyan 2 ( naira miliyan 612).