Adam Zango ya nemi gafarar Ali Nuhu

Ali Nuhu da Adam Zango
Bayanan hoto,

Wasu na ganin rikicin da jaruman biyu ke yi wasan kwaikwayo ne

Shahararren jarumin fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango, ya nemi gafarar jarumi Ali Nuhu a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Sakon mai dauke da wani hoton da ya nuna Zango ya durkusa kuma Ali na zaune bisa kujera, ya zo ne kwanaki bayan Zangon ya wallafa wasu hotunansa da Ali a Instagram bayan sun kwashe kwanaki suna "gaba".

Sakon Adam Zangon ya ce "tuba nake sarki gwiwowina a kasa".

Tuni dai magoya bayan jarumin suka fara tofa albarkacin bakinsu kan hoton da Zangon ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Rayuwar Adam A Zano a takaice

  • An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
  • Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
  • Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
  • Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
  • Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
  • Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
  • Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
  • Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16

Rayuwar Ali Nuhu a takaice

  • An haife shi a watan Maris na 1974
  • Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
  • Ya yi digiri a jami'ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo a 1999
  • Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci
  • Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a fina-fina Nollywood
  • Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya
  • Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa ake masa lakabi da Sarki

Asalin hoton, Instagram

Bayanan hoto,

Wasu na ganin rikicin da jaruman biyu ke yi wasan kwaikwayo ne

Jaruman biyu suna gaba-gaba a masana'antar Kannywood din inda suke da mabiya da dama a shafukan sada zumunta.