Za a mayar da 'yan gudun hijirar Najeriya 56,000 gida

'Yan gudun hijira

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta ce ta kammala shirye-shirye na mayar da 'yan gudun hijirar kasar daga garin Difa a jamhuriyar Nijar zuwa gida.

Shugaban hukumar a arewa maso gabashin kasar, Bashir Garga, shi ya bayyana hakan a wani taron bayar da agajin gaggawa da hukumar ta shirya a birnin Maiduguri ranar Laraba.

A cikin 'yan kwanakinnan dai rahotanni na cewa hukumomi a Najeriya suna kokarin mayar da wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu domin su samu damar yin zabe a babban zaben kasar.

A wani lamari da ya jibinci hakan, rahotanni daga birnin na Maiduguri na cewa annobar amai da gudawa ta bulla a birnin.

Hukumomin lafiya a jihar Borno sun ce annobar ta kashe mutum 14 tare da kwantar da kimanin 400 a birnin Maiduguri cikin makon jiya.

Wata sanarwa da ma'aitar kiwon lafiyar jihar ta fitar ranar Laraba ta ce an samu labarin mutum 380 ne suka harbu da ita yayin da wadansu mutum 14 suka rasa rayukansu.

Yawancin wadanda cutar ta kashe dai sun mutu ne a sansanonin 'yan gudun hijira.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Annobar ta kashe mutum 14, inda yawancin suke a sansanonin 'yan gudaun hijira