Shin ko ina labarin fitaccen jarumi Dilip Kumar?

Asalin hoton, India Today
Da yawa daga cikin ma'abota kallon fina-finan kasar Indiya za su so su ji labarin Dilip Kumar.
Shahararren jarumin wanda za a ce ya taka muhimmiyar rawa sosai a Bollywood, yana nan daram da ransa, sai dai ya tsufa.
Dilip Kumar wanda a shekarar 2018 ya cika shekara 95, an haife shi ne a ranar 11 ga watan Disambar 1922.
Sunansa na ainihi Muhammad Yusuf Khan, kuma Musulmi ne gaba da baya.
Za a iya ce shi ne jarumi da ya fara amfani da sunan Khan a cikin jaruman fina-finan kasar Indiya.
An haife shi a zamanin Turawan mulkin mallaka, inda a lokacin da Turawan Birtaniya ke mulkin kasar Indiya.
Ya yi karatu a makarantar Barnes School, daga nan kuma ya ci gaba da karatunsa.
Ba su jima a garinsu wanda yake a yankin Peshawar, sai kuma suka koma Chembur a yankin Mumbai shi da iyayensa.
Da yake Dilip mutum ne mai sauki kai da kuma saurin sabo, ba su jima ba a sabon wurin da suke ya yi abota da mutane da dama.
Daga nan, sai ya sake komawa Pune, Maharashtra, a nan ne kuma da yake ya zama saurayi, sai ya fara kokarin ganin ya nemi abin yi don ya taimaka wa mahaifinsa.
Yadda Dilip Kumar ya fara fim
Asalin hoton, The Indian Express
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
A shekarar 1942 ne, Dilip Kumar ya hadu da Dokta Masani a wani waje wato Churchgate station, daga nan ne sai Dokta Masani ya bukace shi da ya raka shi zuwa wani kamfanin shirya fina-finai na Bombay Talkies da ke Malad.
A nan ne ya hadu da jaruma Devika Rani, mai wannan waje na Bombay Talkies, wadda har ta bukace da ya sanya hannu a kan kwantiragin cewa zai fara aiki a kamfaninta ya kuma amince.
To anan ne ya gadu da jarumi Ashok Kumar wanda ya ba shi shawarar cewa ya fara fitowa a fim mana, domin ya ga zai iya.
Da farko Dilip na aiki ne a bangaren rubuta labari da tsarawa saboda ya kware wajen iya rubutu a kamfanin, to amma daga bisani sai ita kanta mai kamfanin ma ta ba shi wannan shawara na ya fara fitowa a fim ya kuma amince.
Fim din da ya fara fitowa a rayuwarsa shi ne Jwar Bhata a shekarar 1944.
Wannan fim bai yi wata kasuwa ba, amma a shekarar 1947, a lokacin da ya yi fim din Jugnu wanda ya fito tare da Noor Jehan, shi ne fim dinsa na farko da ya yi fice, wato ya samu karbuwa.
Daga nan ne fa masu shirya fina-finai suka fara rububinsa domin ya yi musu fim.
Ya fara fim ne a lokacin da ake amfani da talabijin marar kala.
Asalin hoton, The Hindu
Dilip Kumar ya kan taka rawa iri-iri a fina-finai, kama daga soyayya da barkwanci da kuma fada.
Ya yi fitattun fina-finai da suka hada da Shaheed da Mela da Andaz da Daag da Devdas da Azaad da Ganga Jamuna da Ram Aur Shyam da Kranti da Karma da kuma Saudagar.
Dilip Kumar shi ne jarumin da ya fara karbar Lakh 1 a fim, kwatankwacin $110,000 a 2017.
Kuma shi ne jarumi namiji na farko da ya fara karbar kyautar gwarzon jarumai na kamfanin Film Fare.
Sannan kuma sau tara yana karbar irin wannan kyauta a kamfanin, hakan ya nuna cewa har yanzu ba a samu jarumi namiji da ya kai shi samun irin wannan kyauta ba.
Har yanzu ba a samu jarumi kamar Dilip Kumar ba a cikin jarumi maza na Indiya saboda irin gudunmuwar da ya bayar a fannin fina-finai na Indiya.
Ya shafe shekara fiye da 60 yana fina-finai.
Wani abu kuma ga Dilip Kumar shi ne, baya ga fitowa a ciki, ya kan shirya shi ko ya rubuta labarin fim, domin shi mutum ne mai son rubuce-rubuce, kuma yana da basira sosai, sannan kuma ya iya harshen Turancin Inglishi sosai, da ya yake a lokacinsu, Turawan mulkin mallaka ne suka koyar da su a makaranta.
Sannan kuma, baya ga harshensa na Hindu, ya iya wasu yarukan kamar Urdu da dai makamantansu, wannan ne kuma ya ba shi damar fitowa a cikin fina-finai bana Hindu kadai ba, har da na sauran yarukan kasarsa.
Wani bangare na rayuwar Dilip Kumar
Baya ga fina-finai da Dilip Kumar ke yi da shirya su da ma rubuta labari, ya taba siyasa, domin har mukami ya rike.
Asalin hoton, EXPRESS
San nan ya sauke faralli ma'ana aikin Hajji, amma sai da ya fara zuwa Umrah a shekarar 2013, da shekara ta zagayo wato a 2014, sai suka tafi aikin Hajj tare da matarsa Saira Banu.
Shima dai Alhaji ne, sannan kuma mai fafutuka ne.
Dilip Kumar ya samu lambobin yabo da dama daga gwamnatin kasar India.
Dilip Kumar shi ne ya yi dalilin shigar wasu jarumai harkar fina-finai a kasarsu kamar Johnny Walker da Mukri da Aruna Irani da kuma Kader Khan.
Asalin hoton, The Tribune
Fitaccen jarumin ya yi soyayya da jaruma Madhubala har tsawon shekara bakwai, amma ba su yi aure ba, daga baya a shekarar 1966 ya auri jaruma, Saira Banu, wadda ya bai wa shekara 22, daga baya kuma ya sake aure inda ya auri Asma Sahiba, amma ita ba su jima tare ba auren ya mutu.
Har yanzu dai suna tare da matarsa ta fari, amma kuma ba shi da da.
Dilip Kumar duk da yawan shekarunsa, ba shida da wani ciwo, illa dai tsufa.
Manyan jaruman Indiya dama 'yan kasar suna matukar girmama Dilip Kumar saboda dattijo ne na kowa, ga kuma suna da ya yi wajen aikin taimakon marassa karfi.
Asalin hoton, Prothon Al English
Asalin hoton, Catch News
Asalin hoton, The Quint