An kori 'yan sandan Najeriya uku daga aiki

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Babban sufeton 'yan sandan kasar ya amince da kora daga aiki da aka yi ma wasu jami'an 'yan sanda uku, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar 'yan kasar DCP Jimoh Moshood ta bayyana.

Ana zargin su ne da shiga gidan tsohon minista Cif Edwin Clarke, ba bisa ka'ida ba, ba kuma tare da izini ba domin gudanar da bincike a ranar Talata, kamar yadda sanarwar ta ce.

Mista Clarke wani na kusa da tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan ne.

Jami'an 'yan sandan dai su ne: Godwin Musa da Sada Abubakar da kuma Yabo Paul.

An dauki matakin korar jami'an ne bayan da aka musu shari'a a wani zama na musamman, a cewar sanarwar.

Sai dai ba a yi karin haske ba game da ko jami'an suna da damar daukaka kara ba.

Hakazalika sanarwar ta ce wanda ya tsegunta wa rundunar bayanan, Ismail Yakubu, ana tuhumarsa a wata kotu kan zargin bai wa rundunar bayanan karya.

A watan jiya ne dai aka sallami shugaban hukumar tsaron farin kaya ta kasar (DSS) Lawal Daura.

Bayan da aka tura jami'an tsaron farin kaya zuwa Majalisar Dokokin kasar ba tare da sanin fadar shugaban kasa ba.