Maras hannu mai digirgir na son ya zama dan majalisa

Maras hannu mai digirgir na son ya zama dan majalisa

Vitalis Lanshima ya rasa hannayensa ne a lokacin da yake yaro, amma wannan larurar ba ta hana shi neman ilimi ba.

Kuma ya samu tallafin zuwa karatu zuwa kasar Amurka a Jami'ar Ballarmine da ke kasar.

Bayan ya gama digiri na daya da na biyu, Vitalis wanda dan asalin jihar Filato ne yana kan hanyarsa na kammala nazarin samun digiri na uku.

Duk da cewa yana aiki a Amurka, Lanshima yana da burin zama dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa a majalisar wakilan Najeriya.